__ Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana abinda ke faruwa tsakanin al'umar Fulani (Makiyaya) da Manoma a matsayin wani shiryayyen abu da bashi da asali, kuma an shirya shi ne domin haɗa rigima tsakanin su. “Naga wani abu da yake gudana yanzu, ina ganin shi a rubuce rubuce da maganganun da akeyi a Facebook. Na farko inda ake ƙoƙarin a haɗa faɗa tsakanin ɓangaren al'umma da wasun su domin kashe juna! Fulani makiyaya, wanda su an san su da shanu kuma shanun nan sune rayuwar su, suna tafiya laifya lau daga wuri zuwa wuri domin suyi kiwon su. Ba'a taɓa samun matsala ba shekara ɗaruruwa tare da su (fulanin). Su suna kiwon su ne, shanun sune rayuwar su.
Ya bayyana cewa suna temakon junan su ne, (Fulani da Manoman) “Domin idan Kaka tayi, Manoma na marhaban da su ne, suzo su sauka a gonakin su su zuba musu taki! Da safe suje kiwon su, Matan su su kawo Nono gari, haka ake zaune shekara da shekaru lafiya lau!” ya nuna cewa da gangan ake so dole sai an haɗa su rigima, yace “To yau anje an dira kan su (Fulanin) an rabasu da shanun an zautasu an basu Bindigogi. Cikin irin zauta mutanen da akayi akwai wanda akaje rigarsu aka kaɗa shanun sai kuma suka kashe matan su. Harma inde sunga tsohuwa zasu iya yadata, sunga wata yarinya-yarinya tana goyo, sai suka fizge goyon suka ce da Mijin wannan Ɗan ka ne? Yace eh, sai suka wurga masa! Wurgawa ya cafe,! Suka tafi da Matar!” ya faɗa. To, mutumin da aka masa haka yanzu anzo an zauta shi an haukata shi, an rabashi da abinda ya sani (Shanu) an kuma bashi Bindiga, kuma anzo ance yanzu sunan shi ɗan ta'adda!.
“Yanzu irin wannan idan mutum ya Haukace menene baze yi ba? To daga nan sai a bashi Bindiga! Bayan an zauta mutum sai a bashi Bindiga, to a na nan sai akace an samar da ƴan ta'adda wai Fulani, duk kashe kashe sai ace Fulani ne sukayi!”. Shaikh Zakzaky, ya bayyana al'umar Fulani a matsayin mutanen da suka fi kowa zaman lafiya, har yake cewa “Inda akwai mutumin da yafi kowa zaman lafiya to sai muce sune al'ummar Fulani” Inji shi. Ya ƙara da cewa; “Na'am duk da na san akwai wasu makiyaya da suke zuwa daga can arewan mu wajan Nijar wanda su ɗabiar su wani iri ne wanda ake ce musu 'Bakolo' idan kaji anyi rigima da Manoma (tsakanin Manoma da Makiyaya) to su ne, amma banda Fulanin da ake zaune da su basa rigima tsakanin su da Manona” ya kara da haka.
Ya tono wani muhimmin abinda ke cigaba da ƙokarin faruwa, wanda yace bayan wancan yanzu kuma ana ƙoƙarin haɗa wata rigimar inda ake son a samar da ƴan ta'adda Hausawa! su kuma su rama akan Fulani. “Yanzu bayan wancan ana ƙoƙarin kauwana (samar) da ƴan ta'adda Hausawa su kuma su rama akan Bafulatani, to, wannan abu da ban al'ajabi (mamaki) in kunji suna wani maganganu, wai su kuma Hausawa ne suna zagin Fulani, har naji wasu suna zagin Shehu Ɗan Fodiyo har da Baban shi” Inji shi. Ya nuna duk wannan sharrin maƙiya ne, “Domin su Maƙiya basa buƙatan mu, domin inda ace gaba ɗayan mu za'a share mu da suna so, inda ace akwai wani 'button' (madanni) wanda idan an latsa duk ƴan arewa zasu baje a nemesu a rasa, wallahi zasu matsa! domin suna so ya zama babu mutane ne arzikin dake ƙarƙashin ƙafafuwan mu suke so” inji shi.
__ Daga Bilya Hamza Dass
0 Comments