Bayan juyin mulkin da Iran ta yi a 1953 , Pahlavi ya hada kai da Amurka da kasashen Yamma don yin mulki da karfi a matsayin cikakken sarki . Ya dogara kacokam kan goyon bayan da Amurka ke samu don ya ci gaba da rike madafun ikon da ya rike na tsawon shekaru 26. Wannan A Wannan Lokacin Idan Kasar Iran 🇮🇷 zata Fitar Da kudi sai Shugaban Kasar Amurka ya sa hannu.
A Iran da juyin juya halin ( Persian : انقلاب ایران , romanized : Enqelâb-e Iran , [ʔeɴɢeˌlɒːbe ʔiːɾɒːn] ), kuma aka sani da juyin juya halin Musulunci ( Persian : انقلاب اسلامی , romanized : Enqelâb-e Eslâmī ) ya jerin abubuwan wanda ya kai ga kifar da daular Pahlavi karkashin Shah Mohammad Reza Pahlavi , da kuma maye gurbin gwamnatinsa da jamhuriyar Musulunci karkashin jagorancin Ayatullah. Ruhollah Khomeini
Juyin juya halin ya samu goyon bayan kungiyoyin islama daban-daban.
Juyin-Juya Halin Kasar Iran wani kokari ne da yan kasar Iran 🇮🇷 suka yi wanda ya basu nasarar hambarar da mulkin sarauta a kasar tare da kafa mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran. A karkashin Juyin-Juya Halin, al’ummar kasar su hambare mulkin Sarki Shah Muhammad Reza Pahlavi tare da nada Ayatollah Ruhollah Khomeini a matsayin jagoran kasar.
An kwashe kimanin shekara daya a gudanar da gwagwarmayar Juyin-Juya Halin Kasar Iran 🇮🇷 wato daga farkon shekarar 1978 zuwa farkon shekarar 1979.
Asalin Juyin-Juya Halin
Kafin faruwar Juyin-Juya Halin Kasar Iran, abubuwa da yawa sun faru wadanda suka janyo Juyin-Juya Halin. Sai dai mafi muhimmanci shine dalili na addini. Domin kuwa mutanen kasar Iran sun kasance mutane masu kishin addini da kyamatar akidun kasashen Yamma.
A cikin shekarar Shekarar 1963, gwamnatin Masarautar Iran karkashin Sarki Shah Reza Pahlavi ta kaddamar da shirin gwamnati akan tattalin arziki, tsarin siyasa, da kuma tsarin zamantakewar al’umma wanda ake kira da ‘White Revolution’. A karkashin tsarin na White Revolution, Sarki Shah ya tsara cewa daga wannan lokacin kasar Iran zata dinga salon tsarin tattalin arziki, siyasa, da kuma zamantakewa irin na kasashen Turawan Yamma da Amurka. Sai dai kuma mutanen kasar Iran sun nuna adawar su ga wannan tsarin saboda sun ce tsari ne wanda yaci karo da addinin Musulunci da kuma al’adunsu. Don haka ne tun daga nan gwamnatin Masarautar Iran ta fara yin rigima da malaman addini da kuma sauran yan kasa.
Haka kuma zuwa tsakiyar shekarun 1970 kasar Iran ta fara fuskantar matsain tattalin arziki. Don haka ne masana masu ilmi, dalibai yan gwagwarmaya, da kuma matsakaitan yan kasuwa suka fara juya wa gwamnati baya. A kwana a tashi ma’aikata suka fara tafiya yajin aiki, wasu daga cikin al’ummar kasar kuma suka fara zanga-zanga. Hakan kuma ya fara alamta cewa akwai yiwuwar faruwar hargitsi a kasar Iran.
Faruwar Juyin-Juya Halin Kasar Iran
Gwagwarmayar Juyin-Juya Halin Kasar Iran ya fara ne a farkon shekarar 1978 a lokacin da dubban al’ummar kasar Iran suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin Masarautar Iran. A hannu daya kuma Shugaban Addinin Musulunci na Iran wato Ayatollah Ruhollah Khomeini wanda yake gudun hijra a kasar Iran yayi amfani da damar wajen bawa yan gwagwarmayar kwarin gwiwa ta hanyar yin jawabai da taimakon kudi.
Zuwa watan December na shekarar 1978 miliyoyin yan kasar Iran sun cika manyan titutuna na babban birnin kasar wato Tehran da kuma sauran manyan biranen kasar. Mutanen kasar sun nuna gajiyawar su ga gwamnatin Sarauta tare da bukatar Sarkin Iran Muhammad Reza Pahlavi da ya sauka daga mulki. Don haka ne a ranar 16 Ga Watan Junairu shekarar 1979 Sarki Shah ya gudu ya bar kasar Iran tare da yin gudun hijra zuwa kasar Masar wato Egypt. Hakan kuma ya kawo karshen Juyin-Juya Halin Kasar Iran.
A daya hannun kuma mutanen kasar Iran sun gayyaci Ayatollah Ruhollah Khomeini Wanda Ke Gudun hijira A Kasar France 🇫🇷 domin ya dawo ya kafa gwamnatin Musulunci.
Don haka ne Ayatollah ya dawo kuma ya zama sabon jagoran kasar Iran wadda ta koma Jamhuriyar Musulunci ta Iran wato a turance Islamic Republic of Iran.
An zargi sojojin Shah kuma sun ba da gudummawa kai tsaye wajen hambarar da shi. Masu lura da al’amura sun bambanta kan adadin mutanen da suka mutu. Gwamnatin Musulunci ta ce adadin mutane 60,000 da aka kashe; Dangane da wannan adadi, masanin tarihi na soja Spencer C. Tucker ya lura cewa "Gwamnatin Khumaini ta wuce gona da iri kan adadin mutuwar juyin juya halin Musulunci saboda dalilai na farfaganda". Akalla masanin tarihi ɗaya a Yammacin Turai ( Charles Kurzman), zana bayanai dalla-dalla daga baya daga Jamhuriyar Musulunci, ya yi imanin adadin ya kusan kusan 2,000-3,000.
Tucker ya bayyana cewa ijma'in masana tarihi dangane da kiyasin mace-mace a lokacin juyin juya halin Iran (daga Janairu 1978 zuwa Fabrairu 1979), adadi tsakanin 532 da 2,781
Daga; Dr. B Salia Sicey
0 Comments