Takaitaccen tarihin Mansa Musa, mutumin da yafi kowa kudi a tarihin duniya da ya fito daga nahiyar Afrika.


Asalin Mansa na nufin Sarki, an bawa Musa wannan suna a lokacin da ya zama Sarkin kasar Mali 🇲🇱 a shekarar 1312 Mansa Musa ya mulki kasashe a nahiyar Afrika da suka hada da Niger 🇳🇪 Chad 🇹🇩 Mali 🇲🇱 Senegal 🇸🇳 Gambia 🇬🇲 An bayyana cewa yawan arzikin Mansa Musa ya kai dalar Amurka biliyan dari hudu ($400b) 💸💸💰Mansa Musa wanda aka fi sani da Musa Keita ya hau kan karagar mulkin kasar Mali 🇲🇱 a shekarar 1312. Lokacin da aka nada shi, an bashi suna Mansa, ma’ana Sarki. 

An ce Mansa Musa ya ci birane 24 da yaki, kowannensu yana da gundumomi da suka kunshi manyan garuruwa da kadarori. Mansa Musa ya shugabanci kasashe da yawa. A takaice ya mulki dukkan (ko sassa) na Mauritania 🇲🇷 Da Senegal 🇸🇳 Da Gambia 🇬🇲 Guinea 🇬🇳 Burkina Faso 🇲🇱 Niger, da Chad 🇹🇩 
Dukiyarsa ta shahara a duniya a lokacin da ya tafi aikin Hajji a shekarar 1324 zuwa garin Makka, wanda ya yi tafiya mai nisan mil 4000

Dukiyarsa ta shahara a duniya a lokacin da ya tafi aikin Hajji a shekarar 1324 zuwa garin Makka 🕋wanda ya yi tafiya mai nisan mil 4000.

An samu labarin cewa yana da kadarori da suka haɗa da mutane 60,000, ciki har da bayi 12,000 waɗanda kowannensu yana daukar sandunan zinare ( Gold ) mai nauyin kilo 4, haka kuma suke shirya dawakai da jakuna.

Musa ya samar da dukkanin abubuwan bukata domin ya ciyar da gaba daya mutanen sa da dabbobinsa. Wadannan dabbobi sun hada da rakuma 80 wadanda kowannensu yake daukar kaya mai nauyin kilogiram 50 zuwa 300.

Musa na bawa talakawa zinarin da ya hadu da su ta hanyar sa. Ba wai kuma kawai ya na kyauta a biranen da ya bi ta kan hanyar zuwa Makka 🕋 ba ne, ciki har da birnin Alkahira da Madina 🕌An ruwaito cewa yana gina Masallaci a ranar kowacce Juma’a.

Musa ya lalata tattalin arzikin yankunan da ya ratsa ta wadanda suka hada da biranen Alkahira, Madina, 🕌 da Makka, 🕋Darajar zinare ta lalace har a shekaru masu zuwa. Farashin kayayyaki sun fadi a wadannan birane. Don daidaita kasuwar zinare, a hanyarsa ta dawowa daga Makka,🕋 Musa yana karbar duk wani zinare da zai iya karba daga masu bada bashi a Alkahira, da kudin ruwa mai yawa.

Tarihi ya nuna cewa wannan ne karo na farko da wani mutum ya daidai ta farashin gwal a kasuwannin duniya.

An bayyana cewa arzikin Musa ya kai dalar Amurka biliyan dari hudu ($400b) 💸💰💸

Daga -: Dr. B Salia Sicey

Post a Comment

0 Comments