Matsala biyar da karancin man fetur ya jawo wa 'yan Najeriya

An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigurɓataccen man da ya dinga lalata ababen hawan mutane, zuwa samun dogwayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matuƙar tsada.

Hukumomi dai tuni suka yi bayanin dalilan da suka sa aka samu yaɗuwar gurɓatacen man, wanda zuwa yanzu an dakatar da sayar da shi.

Amma har yanzu ba su bayar da wani bayani mai gamsarwa na dalilin da ya sa man yake wahala ba.

Sai dai kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yaɗu a kasuwa.

BBC ta tambayi masu bin shafukanta na intanet kan su bayyana halin da arancin an fetur din ya saka su a ciki a yakuna daban-daban na Najeriya.

Kuma daga wallafa hakan a ranar Talata an samu bayanai daga kusan mutum 150 da suka bayar da labaran irin matsalolin da ƙarancin man fetur ya jawo wa ƴan Najeriya.

Bayan bin diddigin bayanan da aka turo, mun gano manyan matsaloli biyar da ƙarancin man ya jawo wa yan Najeriya.

1. Toshe hanyoyi

gidan mai

Layukan a gidajen mai sun yi tsawo fiye da yadda aka saba gani a baya-bayan nan a manyan biranen Najeriya da suka haɗa da Abuja da Lagos, amma duk da haka gidajen mai ƙaɗan ne ke sayar da fetur din.

A manyan birane irin su Abuja mazauna unguwannin da suke maƙwabtaka da gidajen mai na ganin bone, kamar yadda muka samu bayanai daga mutane.

A misali babban titin Murtala Muhammad Way na hanyar Kubwa wanda ke ɗauke da manyan gidajen mai da dama, ya kan cushe da cunkoso saboda motocin da ke kan layuka.

Hakan yana jawo damuwa da matsalar ɓata lokaci ga ma waɗanda ba man za su saya ba.

Ga abin da wasu ke cewa:

  • Tyson: Muna shan wahala man fetur a Gwarimpa Abuja. Don Allah a taimaka fada wa gwamnati Nigeria ta samo mana man fetur a yanzu
  • Usman Abdullahi Adamu: Gaskiya mu a gombe muna cikin wahalar man fetur sosai domin gidajen mai da yawa sun ƙi su bude ɓalle ma mu je mu saya, sannan ga bala'in gosulo.

2. Ƙarin kuɗin abin hawa da tsadar wasu abubuwan

fuel

Kasuwar 'yan bumburutu ta bude

Wata matsala ta biyu da al'umma ke kokawa a kanta ita ce ta yadda masu ababen hawa suka ƙara farashi.

A wasu wuraren ma ba farashin abin hawa ne kawai ya yi tashin gwauron zabi ba, har da na wasu abubuwan yau da kullum, kamar dai yadda wasu suka shaida mana.

Ga abin da wasu masu bin shafukanmu suka aiko mana:

  • Sani Adamu: "E to a suleja inda nike neman abincina da dan dama, to amma har masu Keke Napep sun fara tsauwala kudi.
  • Ismail gambo Ali : Assalamualaikum daga Ismail gambo Ali kwankwaso gaskiya tsadar man fetur ta janyo mana masifar Karin kudin abin hawa a garin na Kwankwaso
  • Tijjani Tukur Turawa: Maganar gaskiya ana fuskantar wahalar mai anan Ikosi Ketu Lagos, domin har ta kai an kara farashin cajin waya daga Naira 50 zuwa Naira 100
  • El bash B Hussain: A yankin Kurna karamar hukumar Dala a jihar Kano abin sai dai mu ce (إِنَّا لِلّهِ وَإِنَّـا إِلَيْهِ رَاجِعونَ) saboda hatta gidan kallo ya koma 200
  • Khady: Abun ba Dadi,qarancin Petro ya hanani zuwa school saboda babu ababen hawa kowa Yana gidan Mai layi,anata rugingimu a gidajen mai.

3. Yini da kwana a layi

Babban tashin hankalin da ƙarancin rashin mai ya jawo wa ƴan Najeriya shi ne shafe lokaci da suke yi a gidajen man.

A wasu lokutan ma bayan mutum ya yini ya kwana, da zarar layi ya kusa zuwa kansa sai a ce man ya ƙare.

Wannan lamari na matuƙar tunzura mutane. Ga abin da wasu da dama ke cewa.

  • Abba: Yanzu haka a layin gidan mai nake kusan motoci dari biyar ne a gabana
  • Sabitu Sale wakili: Mu dai anan jihar Kano wasu kadan ne suka bude kuma suke ba da man futur da sauransu amman sai dai layi, don kai ka ce taron arfa ne
  • Nura Ali Warure: Akwai karancin Petrol a birnin Kano, abin ya kai matuka ba za ka samu man fetur ba sai ka shafe sa'o'i a dogon layi
  • Mubarak Ibrahim: A nan jihar Lagos tun jiya nake kan layi bada mai amma har yau ban samu ba, gaskiya muna bukatar gwamnati tayi gaggawar daukar mataki.

4. Tsadar man fetur - Ko da kuɗinka sai da rabonka

Lamarin man fetur ya zama ko da kuɗinka sai da rabonka. Tadarsa ta yi yawa ta kai intaha kamar yadda mutane da dama suke kokawa.

A wasu wuraren ma sai dai a sayi mai a hannun ƴan bumburutu, wadanda suke nunka kudin kowace lita sau uku ko huɗu kan yadda aka saba saya.

Ga bain da wasu suka shaida mana:

  • Babangida Sulaiman Abdulkareem Mashegu: Gaskiyar magana a nan ita ce, mai a yankinmu, yayi tsada ki tana Naira ɗari shida da hamsin, a nan Kuje Abuja Nigeria
  • Ishaka lawal : Gaskiya kam munashan wahala sosai sakamakon rashin man fetur a yankimmu yanzu haka munashan litar man fetur #500 a garinmu na jibia hakama
  • Hasheem muhammad zak: Wlh wahalar man fetur take a yankunanku a gaskiya muna fah ma da wahala man f
  • etur yanxu haka lita daya a naira 500 kasaya ko kabari ba ma m
  • Mudassir: Munaciki matsanacin wahala mai Wanda saikayi away uku ko hudu bakasamu maiba idan kasamu a black market to galan daya 3000
  • Usman Hussaini: Wallahi muna shan wahala sosai abun ba a magana, saboda yanzu haka wallahi litar mai 600 ake sayarwa a inda nake wato jihar Kaduna unguwar RIGASA
  • Fodio Muawiyyah Bodinga: Sokoto Yau Litar Mai Takai N300 Black Market N400. Allah Yayimana Sauki Wannan Masifa,ya Agajemu. Amin
  • 5. Dambe da zage-zage

    fuelWasu gidajen man sun zama sansanin faɗa

    Wannan shi ne abu mafi ɓata rai dangane da matsalar ƙarancin man.

    Wasu gidajen man sun zma kamar filin dambe da kokawa duba da yadda faɗa ke rincabewa tsakanin masu saye da ke kan layi, sakamakon musun na riga ka, ko na ka sha gaba na.

    Rabon faɗa ya zama shi ne babban abin da aka fi mayar da hankali a kai a wasu gidajen man. Har ta kai wasu gidajen kan rufe su dakatar da ba da man har sai komai ya lafa.

    Matashiya

    Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arziƙin man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwaman shekaru tana fama da samun matsalar ƙarancin man fetur akai-akai


    Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a ƙasa


    Wannan ne dalilin da ya sa a dole ƙasar ke sayo tataccen man fetur daga ƙasashen wajen da take sayar musu da ɗanye


    Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarnaƙi a wajen samar da ma


    Amma kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yadu a kasuw


    A yanzu NNPC ya ce yana shirin samar da lita biliyan 2.3 na fetur a fadin ƙasar - kuma cibiyoyin NNPC ɗin za su fara rarraba man ba dare ba rana a fa din ƙasar don samar da sauki.

source: BBCHausa

Post a Comment

0 Comments