Falala da Ayyukan Watan Sha'aban Mai Albarka


Falala da Wasu Daga Cikin Ayyukan Da Ake Son Aikatawa a Wannan Wata.

Da farko yana da kyau a san cewa watan Sha'aban wata ne mai girma da daukaka da aka jingina shi ga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka, an ruwaito cewa Manzon Allah (s) ya kasance ya kan azumci dukkan watan da kuma gama shi da watan Ramalana mai alfarma. Manzon Allah (s) yana cewa:

"Sha'aban wata na ne, duk wanda ya azumci rana guda cikin watana zai shiga Aljanna".

An ruwaito Imam Sadiq (a.s) yana cewa:

"Idan watan Sha'aban ya shigo, Imam Sajjad (a.s) ya kasance ya kan tara sahabbansa ya ce musu: Ya Sahabbaina shin kun san wannan wata kuwa? Wannan watan Sha'aban ne da Manzon Allah (s) yake cewa: Sha'aban Wata na ne, don haka ku azumci wannan wata don kaunar Annabinku da kuma neman kusanci da Ubangijinku. Ina rantsuwa da wanda raina ke hannunSa, na ji babana Husain (a.s) yana cewa: Na ji Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Duk wanda ya azumci Sha'aban don kaunar Manzon Allah (s) da kuma neman kusanci da Ubangiji, Allah Zai so shi kuma Ya kusata shi da karamarSa ranar Lahira, sannan kuma Ya sanya shi cikin Aljanna".

Al-Sheikh ya ruwaito daga Safwan Al-Jammal yana cewa: "Imam Sadiq (a.s) ya gaya min cewa: Ka kwadaitar da na kusa da kai kan azumin watan Sha'aban, sai na ce masa: Ya Shugabana shin akwai wani abu (wata falala) ne a cikinsa. Sai ya ce: "Na'am, Manzon Allah (s) ya kasance idan ya ga watan Sha'aban, ya kan umurci mai shela ya shelanta cikin Madina yana cewa: Ya ku mutanen Madina, Ni Manzon Allah ne a gare ku. Ku sani cewa watan Sha'aban watana ne, Allah Ya yi rahama ga wanda ya taimake ni a watana. Daga nan sai ya ce: Amirul Muminina (a.s) ya kasance ya kan ce: "Ban taba barin azumin watan Sha'aban ba tun daga lokacin da na ji wannan mai shela na Manzon Allah (s), sannan kuma azumin Sha'aban ba zai kubuce min ba da yardar Allah. Sannan kuma ya kasance yana cewa: "Azumtar wadannan watanni biyu a jere tuba ne ga Allah.

Rubutawa; Muhammad Auwal Bauchi

Post a Comment

0 Comments