Ranar Asabar da safe mun tafi Husainiyya saboda akwai bikin sanya tuta don murnar zagayowar ranar haihuwar Manzo Allah (SAWA).
An tsara musanya tutar Ashura da ta Mauludi. Kuma muna daga cikin masu shirya taron. Ba a ko jima ba kafin nan, muka ji karan jiniya, yayin da muka yi ayari zuwa waje sai muka ga sojiji da makamai suna tsaye a gaban Husainiyya. Wasu mutane suka je don tambayar dalilinsu na girke sojojin, sai suka ce wai sunzo daukar hullarsu ne da ta fadi. Saidai ba a gamsu da amsar ba...
Bayan sunja baya kawai suka fara harbi, sai aka umurce mu da mu koma daga ciki. Yayin shiga cikin Husainiyya sun kashe wasu adadin yan uwa.
Ana kwaso gawarwaki zuwa ciki a lokaci guda kuma sojojin na cigaba da kwashe wasu bayan sun kashe su.
Bayan haka suka turo wasu sojojin cikin Husainiyya a lokaci guda mun lura da suna kara karo karfi. Suka cigaba da harbi yayin da suke kewaye Husainiyya. Da harbin ya ragu zuwa tsakkiyar dare sai suka sanya lasifika suna umurtarmu cewa duk wanda ya rage a cikin Husainiyya ya fito ko kuma su sanya karfi su shigo ciki. Suna iya hangen wasunmu daga nesa, sai ya zama addu'armu a lokacin shine daukewar wutar da ke haskamu. Ana nan sai suka yi amfani da wani nau'in haske daya haskake dukkanin Husainiyyar.
Duk da tabbacinsu na cewa bamu dauke da makami amma hakan bai hanasu amfani da gurneti a kanmu ba. Bayan sun lalata ainihin gate din shigowa tare da wasu kofofin, sai ya zamana sun shigo da karfin gaske suna harbi akan mutanen dake sallah tare da masu rauni dake a kwance. Haka sukai ta Harbin mutane wasu nan take suka cika.
Da gari ya waye suka watsa fetur a cikin Husainiyya sannan suka kunna wuta ya kama ko'ina. Yaran dake ciki nata kuka sojojin basa ko tausayawa, yarannan da damansu 'yan kanana ne kuma yan Islamiyya.
Gashi yaran duk sunyi rauni ga tsananin yunwa dake damunsu, ga tsoro da ya hanasu bacci saboda irin karan makaman da sojojin suka yita harbawa. Sannan yaran nan kuma suna kallo ana kashe sauran yara 'yan uwansu a gabansu.
Na fidda wasu yaran zuwa wani gini dake nan kusa da Husainiyya inda na boye su, amma hakan bai hana sojojin sawa ginin da yaran suke ciki wuta ba. Sam basa tausayin yara, wani soja na kokarin harbinmu sai dan uwansa ya dakatar dashi, hakan yayi sanadiyar kubutarmu daga wutar.
Sannan a nawa bangaren kuma sojojin sun kashe min yarinya. Sannan bayan mun kubuta daga wutar, wasu sojojin na boye inda suka tsaremu kuma sukace mu cire hijabanmu. Amma naki ina fada masu cewa shiga ce ta addininmu, suka amsa mun a fusace tare da duka mai tsananin gaske, wani soja daga ciki ya sanya marikin gatari ya doke ni ta baya, daga nan suka dauremu suka jamu a kasa sannan suka jefamu cikin motarsu tare da kananan yara da gawarwaki inda suka tafi damu bariki.
Sun azabtar damu sosai yayin da muka isa bariki, wata soja tayi ta mari na har sau biyar, wani kuma yayita duka na har saida na daina gani, daganan suka watsamu cikin wani wurin wankan mai kazanta da basu amfani dashi. A nan muka ga wasu almajirai masu kananan shekaru da aka kamo kafinmu. Inda almajiran suka bayyana mana cewa suna bacci ne aka kamosu, zasu kai akalla su talatin.
A tare damu kuma yara ne yawanci masu kananan shekaru wadanda ke dauke da harbi wasu kuma duka. Ban taba tunanin mutum zaiwa dan uwansa irin abinda suka mana ba. Sun yi amfani da kalaman batanci don su bata mu, suna cewa kuma mun tare ayarinsu (mun tare masu hanya). Wannan duk abu ne daya faru a gabanmu, babu wanda ya tare masu hanya kuma Allah zai mana sakayya.
Daga Littafin " Zaria Massacre Survivors Acount"
0 Comments