KARATUN ALQUR'ANI :- Wannan wata na Ramadan ana so mutum ya yawaita karatun Alqur’ani a cikinsa, in son samu ne a duk kwana ukku mutum ya sauke,wato kullum yayi izu 20, in kuma haka bai samu ba to sai yayi abinda ya samu, fata dai mutum yayi sauka a cikinsa fiye da sauran watanni, ya zo a tarihin Imam Khumaini cewa a watan Ramadan ya kasance yana sauke Alqur’ani a duk kwana ukku.Haka nan kuma ana son mutum ya karanta suratul-kadri wato Inna-anzalnahu sau dubu kowane dare. Haka nan ana son mutum ya karanta suratu-Dukan shima kowane dare na watan Ramadan da dai sauransu.A takaice dai hasara ce babba ga mutum a ce watan Ramadan ya kama har ya fita mutum bai sauke Alkur’ani ba wato dai akalla mutum ya samu ya sauke Alkur’ani ko da sau daya ne.A
AZKAR :- Ana so mutum ya yawaita zikirori a watan Ramadan kamar su hailala, tasbihi, istigfar, salatin Manzon Allah (S) da dai sauransu.Wato dai mutum ya yawaita azkar a cikin watan fiye da sauran watanni, saboda wata ne da ake nunnuka ayyuka na bayi, kuma watan Ramadan fursa ce zahabiyya da bai kamata mutum yayi wasa da ita ba, kuma mutum bai sani ba ko wannan shine watan Ramadan na karshe a rayuwarsa, mutum yayi tunanin wasu daga cikin ‘yan uwansa na addini ko na jini ko makwabtansa wadanda watan Ramadan na shekarar da ta wuce dasu mukayi amma na bana bamu tare dasu saboda haka yana da gayar muhimmanci mutum ya ribaci wannan lokaci mai tarin albarka da muke ciki.
ADDU'O'I :- Wannan wata na Ramadan yana da addu’oi da aka ruwaito fiye da sauran watanni, kuma wadannan addu’o'i akwai wadanda ake yin su da daddare, akwai kuma wadanda ake yi da rana,akwai kuma wadanda ake son yinsu bayan kowace sallah ta farilla, akwai kuma wadanda ake yi bayan kowace raka’a biyu ta nafilfili dubu da aka ambata a sama, akwai kuma wadanda ake yin su lokacin as-har wato kafin ketowar alfijir da dai sauransu.To ana so wadannan addu’oi baki daya mutum ya lizimci yinsu tun daga farkon watan Ramadan har karshensa, kuma wannan abu mai yiyuwa ne,misali mu dauki addu’ar da tafi su tsawo duka a watan, wato Addu’ar Abu Hamzatus-sumali wanda ake karanta ta a lokacin Ashar, to akwai bayin Allah da suka haddace ta, kowane dare da ita suke kunutin sallar wutiri.
A takaice ga mai bukatar ganin wadannan addu’oi daban-daban da ake yi a watan Ramadan yana iya duba littafin Ikbal na Sayyid ibn dawus ko mafatihul jinan ko kuma littafin Minhajul Jinan na Ayatullahi Sayyid Abbas Al-kashani, littafi ne da baki dayan sa ya kunshi ibadodin watan Ramadan ne saboda haka yana da gayar muhimmanci mallakarsa domin ana samun littafin, saboda a iya binciken da na yi ban ga wani littafi da ya tattaro ayyukan watan Ramadan ba kamar shi.
ZIYARORI :- Mustahabbi ne ziyarar Imam Husain [AS] daga kusa ko nesa a daren farko na watan Ramadan, da daren sha-biyar da kuma daren karshe, ko da mutum bai samu karanta ziyara kebantacciya ba ta ta wadannan darare to idan yakaranta ziyarar Ashura a dararen to ya wadatar.
Haka nan ziyarar Imam Ali [AS] a daren 21 da dai sauransu.Yin wadannan ziyarori a irin wadannan munasabobi yana da falaloli da kuma fa’idodi masu yawa,daga cikin wadannan fa’idodi shine yana kara kusanta mutum ga Manzon Allah (S) da kuma Ahlul bayt[AS].
INFAKI :- Wannan wata na Ramadan ana so mutum ya yawaita sadaka da kyauta da kuma ciyarwa ta fuskoki daban daban kuma ga mutane daban daban, yazo akan cewa babu wani wata wanda Manzon Allah yake yawaita infaki kamar watan Ramadan.Saboda haka ana so mutum ya yawaita sadaka da kyauta ga ‘yan uwansa na jini da na addini da kuma makwabta da dai sauransu,muna da kyakkyawan misali daga jagoranmu wato Sayyid Zakzaky[H] yadda yake ciyarwa ta fuskoki daban daban musamman ga makwabta a cikin wannan wata na Ramadan.
RAYA DARARE :- Ana so idan mutum zai iya ya raya dararen watan Ramadan baki dayansa, idan kuma ba zai iya ba to sai ya raya wasu daga cikin muhimman darare a cikinsa kamar daren farko, daren 15,19,21,23 da kuma daren karshe.
Raya dare anan ana nufin ya kasance baki daya daren mutum bai yi barci ba,wato ya shagaltu da ibadodi daban-daban. Idan mutum ya bibiyi tarihin wasu bayin Allah zai ga wasu sun kwashe shekaru 40 suna raya dararensu da ibadodi wasu sama da haka, ba mamaki mutum yaga wahalar abun, amma jikin mutum yana da wata dabi’a shine duk abunda ka dora shi akai ko ka saba masa to zai ginu akai, kafin mutum ya saba zai iya shan wahala, amma jikin na sabawa shike nan.
Daga cikin siffofin ibadur-Rahman shine cewa suna raya dare da ibada.
WANKA :- A duk watannin Musulunci babu watan da yake da wanka na shari’a kamar watan Ramadan,saboda mustahabbi ne a daren 1,3,5,7,9,11,13,15,17,19 mutum yayi wanka,ana so kuma tun daga daren 21 har ya zuwa daren 30 kowane dare mutum yayi wanka.Wanka anan shine shigen yadda mutum yake wankan Jumma’a.Yana da muhimmanci mutum yaga cewa bai rasa ko daya daga cikin wadannan wankan ba,saboda yinsa yana da falaloli masu yawa.
©Muhammad Sulaiman [Tambihi]
Daga-: Zauren F-fighters A'amal.
0 Comments