Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da kungiyar daliban jami'a da wakilan kungiyoyin dalibai a birnin Tehran a ranar jiya Talata.
Jagoran ya yi ishara da matakin da wasu kasashen musulmi da na larabawa suke dauka kan kulla hulda da gwamnatin Isra'ila da sunan yin amfani da hakan domin taimaka wa Falastinawa, yana mai bayyana wannan matakin a matsayin babban kuskure.
Ya ce: "Abin takaici, gwamnatocin musulmi suna yin abin da ba shi ne ya dace da su, domin ba sa son yin magana game da batun Falasdinu da gaske. Wasu daga cikinsu na tunanin kulla alaka da yahudawan sahyoniya hanya ce ta taimakawa Palastinu, alhali wannan kuskure ne babba,” in ji jagoran.
Ayatullah Khamenei ya ce irin wannan zaman lafiyar ba zai haifar da wani sakamako ba hatta ga gwamnatin Tel Aviv, yana mai bayyana fatan cewa nan ba da dadewa ba al'ummar Palastinu za su kwato yankunansu tare da 'yantar da masallacin Al-Aqsa daga mamayar Isra'ila.
Jagoran ya yabawa al'ummar Palasdinu, inda ya ce ana zaluntarsu hakikanin zalunci, amma kuma su masu karfin zuciya da juriya ne, wadanda suke baiwa Falastinu kariya ta hanyar tsayin daka da sadaukarwa.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya kuma ja hankali kan sabon tsarin duniya da ake kafawa, wanda a karkashinsa ne Amurka ta ci gaba da rasa madafun iko.
"A yau, duniya tana kan bakin kololuwar wani sabon tsari na kasa da kasa wanda ya kasance yana kan aiwatar da tsarin duniya na biyu da kuma ka'idar tsarin duniya bai daya, wanda a cikinsa, ba shakka, Amurka tana kara rauni a kowace rana.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da jaddada muhimmancin samar da tunani mai zurfi kan rikicin kasar Ukraine bisa sabon tsari da ya kunno kai a duniya.
"Dole ne a yi la'akari da abubuwan da suka faru na yakin na Ukraine da zurfin tunani, kuma a cikin yanayin samar da sabon tsarin duniya wanda zai iya biyo bayan matakai masu wuyar gaske,"
A cikin irin wannan sabon yanayi mai sarkakiya, Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, wajibi ne dukkanin kasashe ciki har da Jamhuriyar Musulunci ta Iran su kasance cikin wannan sabon tsari ta fuskar na'urori da manhajoji don tabbatar domin a ci moriyarsu a dukkanin bangarorin da ake bukatan hakan.
0 Comments