Masu bibiya tare da nazartar karatuttuka da jawaban Sheikh Zakzaky idan baku manta ba a shekarar 2013 wajen taron bikin tunawa da gwarazan musulumci (yaumus shuhada) a Zaria, Sheikh Zakzaky cikin jawabinsa ya bayyana dalilai tare da hakikanin manufar wadannan kashe-kashe da ake a kullum da suna Boko Haram, kidnappers, bandits dasauransu musamman a arewacin Nigeria kamar haka;
Tsakanin zamfara zinari ne ke kwance, suna so su share ariyan da zinarin yake ne ya zama ba mutum ko kadan suyi filin jirgin sama suyi sansanin soja su rika kwasan dukiya.
Nan tsakanin Zaria da Birnin Gwari zinari ne ke kwance da duwatsu masu daraja, so suke su share mutanen wurin su kafa filin jirgin sama su kwasa.
Tsakanin Sokoto har zuwa Borno daga uraniyom (uranium), sai zinari, sai pilatiniyom (platinum), shi suka zo diba. To kuzo mana ayi ciniki (koda ma ku bamu kaza mu baku rakumi ne), amma ku barmu da ranmu kuma ku kyale mana addininmu.
Amma menene na cewa zaku shigo ne da yiwa mutane wayayyu babarodo? Ina kuke da wayon? Yaushe akayi ba'amerike? Yaushe aka yi bature ma tukunna? Wani wayo yake dashi? Eh mana! Dauko tarihin bature ka karanta mana. Badaje, maye, dan bori, yaushe ya waye da har zai mana wayau? Rashin kunyan banza kawai. Kuzo ayi ciniki kunada bindiga mun sani kun iya kisan kai, amma a kyale mana addininmu.
Sheikh Zakzaky ya dauki awanni a wannan rana Inda ya cigaba da fallasa makircin gwamnatin Amarica da Ingila na sabunta sabuwar mamayar nahiyar Africa a karo na biyu, ya kuma ambaci shirin nasu da sunan "Second scramble for Africa" cikin takaici da bacin rai tare da kira ga dukkanin al'ummar Nigeria akan su fahimci cewa lallai wadannan kashe-kashen da ke faruwa shiryayen al'amari ne daga waje tare da zartarwarwar gwamnatin Nigeria.
©Freedom Fighters Ng.
0 Comments