Sojoji sun zuba mana fetur sannan suka sa mana wuta


-Daga Muhammad Altine

Sojoji ne suka harbe ni a kafata. An kaini gidan jagora inda aka kula da lafiyata. Ina kwance a tsakanin gawawwaki sai sojojin suka shigo suna harbin wadanda ke da rauni. Bayan tabbatar da sun kashe kowa, sai suka saka mana wuta; a ranar lahadi kenan. A duk lokacin da wutar ta mutu, zasu sake kunna wata. Sun yi hakan akalla sau hudu. Wannan ne ya sa na samu kuma daga kafa zuwa baya na.

A lokacin ne suka ba mutanen gari damar zuwa satar abubuwan da suka rage mana na daga wayoyi da kudi, amma a zahirin gaskiya suma sun taimakawa sojojin wurin kai gawawwakin wanda suka rasu zuwa kan titi. Lokacin da suka saci kayan wani da ke kwance a kusa dani, sai suka ji ina numfashi. Sai suka ce "Bar mu fada ma sojijin su karasa shi." Sai na roke su da su fitar da ni. Sai dayan su yace "da alama wannan ya wahala sosai!" sai suka tausaya mani. Sai suka ce na yi kaman ina taimaka masu wajen cire gawawwakin, ta yadda zasu samu damar kubutar da ni. Sun ce na je na nimo baro (wheelbarrow) ina tafiya sai suka nuna mani wata hanyar da zata kubutar dani. A haka  dai Allah Ya kaddara cewa zan fita.

Ina samun sauki sosai kuma ciwukan da naji sun kara tabbatar min muna kan hanyar gaskiya. Manzon Allah (SAW) shima ya ga jarabawowi kala-kala, haka kuma sauran Imamai. Manzon Allah da sauran A'imma har zuwa kan Imam Hassan Al-askary duka sun rasu ne a matsayin shahidai. Ba daya daga cikin su (A'imma) da yayu mutuwar gado.

Ina kira ga mabiya Shaikh Zakzaky da kada su gaji da yi masa Addu'a. Allah (SWT) Ya kare shi daga sharrin makiya! Ina kuma kira ga 'yan uwa akan mu samu sabati a Harka Islamiyya, wacce muke kokarin karewa. Abin da ak yi mana lallai makirci ne (wanda makiya suka kitsa).

© Daga littafin "Zaria Massacre: Survivor's Account"

Post a Comment

0 Comments