Zaria Massacre | Yadda Soja Yabudema kananan Yara Wuta Yakashesu Duka.


- Rabi'atu Muhammad

Muna a cikin Hussainiyya lokacin da muka ji an hura usur sau biyu. Ba mu taba jin irin wannan usur din ba. Da muka fito waje, sai muka ga sojoji a motoci jibge. 

Da aka kara hura usur din, sai sojojin suka sauka daga kan motocin su, sai na koma na fadawa yan uwan dake ciki cewa sojoji ne, suke hura usur din, suna dauke da makamai kuma motar da ta kawo su ta koma.

Wasu daga cikin brazu sai suka same su suka tambaye dalilin zuwansu. Sai suka ce suna neman hular su ne (ta sojoji).

Wasu daga cikin yan uwan sai suka roke su da su juya tunda ba su ganta ba. Sai suka koma baya suna fadin ai ai akwai faretin da za'a yi, hakan ne yasa aka ajiyesu a unguwar. Sai yan uwan suka musanta hakan, suka ce musu Husainiyya ko kadan ai bata ma kusa da barikin sojoji kuma basu taba ajiye sojoji ba in har zasu yi Faretin nasu. Sannan suka roke su da su koma.

Sai suka juya zuwa wajen hanyar jirgin kasa aka kuma raka su zuwa filin polo kafin daga baya su sake dawowa. Wasu daga cikin yan uwan sun sake samun su, nan take sai suka raba position suka fara harbi. Suna harbin ne ba kakkautawa mu kuma muna fadin Labbaika Ya Rasulullah! Labbaika Ya Ali!

Ta haka ne suka fara harbi a ranar asabar da misalin karfe 12 da rabi na rana har zuwa lahadi. Bayan sun rusa Husaainiyya da bama-bamai, sai sojojin suka shiga ciki suna harbin duk wanda ke kwance, mai rai ko wanda bai da rai; ko da ko yaro ne, namiji ko mace. Mu a daya bangaren, sai muka shiga wani gida dake kusa da Hussainiyya, sai ga wani soja ya shigo yana harbi. Ni an riga da an harbe ni kuma zafin harbi ya mamayeni, har zai kara harbi na sai daya daga cikin sojojin yace masa ya kyale ni.

Naji sojan na fadin cewa Shi'a ba musulunci bane,  sannan kuma wai ana basu lada ne idan sun kashe yan shi'a, Ya rantse cewa Allah zai basu lada kan abinda suka aikata.

Kananan yara suna neman mafaka a cikin wani daki dake kusa da babbar kofar gidan sai wani soja ya balla kofar ya shiga, shigarsa ke da wuya sai ya bude wa yaran wuta. "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un (Crying)." Wadannan yaran an kashe su ne da harbin bindiga! Sai suka kwashe mu zuwa Bariki, sannan suka azabtar damu. Suka sanya mu dole muka kwanta a kasa kan titi, suna mana izgili da cewa "Shia ba Addini bane, hanyar bata ne!" Suna ikirarin cewa ko sun kashe mu lada suke samu a wurin Allah na abin da suka yi. Sun kwace duka kayayyakin mu sannan suka cire mana Hijabai: suka rufe mana idanuwa, suka sace duk wani abu namu kuma cikin jin dadi suka daddauke mu hoto da wayoyin su ba tare da Hijabi ba.

Basu bar mu munyi barci a wannan ranar ba. sun cigaba da azabtar da mu kafin su cusa mu cikin wata mota da safe. Sun saka mana Teargas a cikin motar wanda ya saka mu tari a gaba dayan tafiyar har zuwa Kaduna.

Wadanda ke da raunuka a jikin su an barsu ne cikin kunci ba kulawa, bana ma iya tsayawa da kafata. Wasu daga cikin matan akwai masu ciki kuma suna da harbi a jikin su. Bayan kulle mu a Kaduna na wasu kwanaki, sai aka sake mu.

Daga Littafin "Zaria Massacre Survivors Account"

Post a Comment

0 Comments