Shekaruna 36. Ina da mata daya, da 'ya'ya biyu. Ina da darajar karatu ta NCE. Ni dan kasuwa ne. A PZ Zariya nake kasuwancina. Wannan wakia ta same ni ne ranar Asabar 12/12/2015. Da misalin karfe sha biyu na rana ne, na dawo daga kauye, sai na biyo taTudun Wada. To, dama ina sana'ata ne a PZ. A Tudun wada ne wasu 'yan'uwa suka shaida mani cewa Husainiyya babu lafiya. Akwai sojoji a wajen. Sai na ce a sayo mani abinci. Sai suka ce, ba sai na ci abinci ba. In wuce Husainiyya kawai.
To, sai na nufi Husainiyya da mashin dina. Tun a PZ na fara ganin Sojoji kowannensu rike da bindiga cikin shirin harbi. Domin in ka saba da hulda da soja, idan akwai alamun harbi ga soja kana iya ganewa. Na cimma 'yan'uwa suma sun yi cirko-cirko a cikin sojojin. Su ma suna muzurai a cikin sojojin. A gefe guda kuma ga jama'a yan kallo. Su ne ma suka tsaida ni. Na hangi kofar Husainiyya cike da Harisawa. Na nemi waje na faka mashin dina. A nan ne na hangi wasu Harisawa sun zagaye wani kwamandan soja. Yana magana da su da Hausa. Amma a gaskiya ban ji abin da yake fada musu ba, domin kafin in karaso ya gama magana. Amma na ji Harisawa na cewa kada a bari ya fita shi kadai. Domin in ya fita shi kadai yana iya bada umarni a bude wuta.
To, da ma tun kafin in zo an ce sun ma bude wuta. Sun ma kashe wasu 'yan'uwa sun wuce abinsu. Dawowa suka yi. To, da ma ka san abin imani ne. Kai ba ka kai imanin wani ba, wani bai kai imaninka ba. A gabana na ga wasu 'yan'uwan da suka kwakkwanta a kan titi. Suka ce ba za a kai ga Husainiyya ba, sai dai in za a tattaka su ne. To, ni a lokacin ina daga baya ina tsaye. A nan ne aka shaida mani cewa ai sojojin suna daukar duk abin da ke faruwa a kyamara ta bidiyo. Tun daga nan na san akwai makircin da suke shirin kullawa. Na ce za su bude wuta ne.
Domin a ka'idar soja in ka ga yana daukar bidiyo, to akwai wani abu da yake so ya yada wa duniya ne cewa ga abin da aka yi masa, shi ya sa ya bude wuta. Ana cikin haka sai na fara jin harbi. Alokacin akwai Sayyid Ali, da Sayyid Humaid, 'ya'yan Sayyid Zakzaky (H). To, sai muka ce a yi kokari a dauke su. Domin kada a maimaita abin da ya faru a Kudus.
To daga nan ne aka dauke su. Ni kuma sai na tsaya a kan titi. Ina tsaye sai na ci gaba da jin harbi. Sai muka fara kwakkwantawa a kasa. Muna kwance, sun share sama da mintuna talatin suna harbi. Sai karar kala-kalar bindigogi kake ji. A nan ne muka hangi ashe tuni sun mamaye filin Polo. Sun kwakkwanta a cikinsa. Sai harbi suke yi daga filin Polo zuwa Husainiyya. Hakan ya tabbatar da cewa ba wai maganar tare hanya ba ce. Saboda rashin imani duk yan'uwan nan da suka kwakkwanta a titi suka ce ba su yarda a wuce Husainiyya ba, haka suka yi ta harbe su daya bayan daya. Kuma mazansu da matansu. Duk suka kashe su. A lokacin ni ina wajen da 'yan tijara da ba 'yan'uwa da suke kasa kaya. To, ina wajen, wannan ledar da suke sanyawa ita ta hana sojojin su gan nj. Ni kuma ina ganin duk ta'asar da suke yi.
Idan sun harbi mutum ya fadi, sai surugo da gudu su sake harbin sa a kai, ko a kirji. A gabana Fatima, yarinya karama, 'yar Alh. Uncle mai abinci, wani soja ya yi kwallo da ita, ya harbe ta. Sai Babanta ya rugo zuwa wajenta. Shi ma suka harbe shi. Haka suka dinga harbe 'yan'uwa da makamai marasa adadi. Agabana motocin sojojin suka dinga wucewa. Wasu na kaucewa gawawwakin da ke warwatse a kan titi. Wasu kuwa sun rinka take gawawwakin ne da motocinsu suna wucewa. A lokacin ne sojojin da ke duke suna harbi suka hango ni a inda nake 6oye. Sai suka yo kaina. Sai na tashi na yi cikin tashar jirgin kasa a guje. Suka ci gaba da harbina. Ina cikin gudu sai na fadi. Tashin da zan yi sai suka same ni. Sun harbe ni harsashin ya shiga ta kafadata, ya fita ta wuyana. Sai na sake fadi. Amma sai Allah ya taimake ni na sake tashi. Na shiga cikin tashar jirgin kasa. A haka ma suna biye da ni. Domin so suke su kashe ni. Allah ya taimake ni, na tsere musu.
To, ashe akwai 'yan'uwa a cikin tashar jirgin. Sai suka rika ni. Ga riga ta fara duk ta jike da jini. Ga shi babu dama a shiga gari da ni. Aka shiga da ni cikin tashar jirgin. Aka bi dani ta kasuwar Sabon Gari a mashin. To, sai jini yana ta zuba daga jikina. Sai aka sani a keke Napep. Aka bi da ni ta Commercial'. Aka biyo da ni ta Shika dam. Aka zagayo dani har ta Mangu. Aka shigo da ni har ta Dam.Aka biyo dani ta Ban Zazzau. Muka bullo ta Kofar doka. Da muka zo Kofar doka ne, sai na ce wa Harisawan da ke dauke da ni, don Allah su kai ni Gyallesu. Domin ni gidan Malam nake ji. Domin na san sojojin za su iya zuwa gidan Malam (H). Domin da ma Sayyid Zakzaky (H) ya gaya mana cewa, suna iya kawo hari ko kafin Tattaki, ko lokacin Tattaki, ko kuma bayan Tattaki. Don haka a lokacin ni gidan Sayyid (H) kadai nake ji. To, dai sun ci galabaa kaina. Suka ce ba za su kai ni gidan Malam (H) ba.' Centre za su kai ni. To, da yake sun fi karfina, kuma su ke dauke da ni, sai na amince. Aka je da ni 'centre'. Aka hada ni da wani dan ISMA. To, da ma shi kadai ya ragea wajen. Sai ya ba ni taimakon gaggawa.
To, ina nan kwance, sai Harisawa suka ce tunda ba mu da yawa, bai kamata a bar mu a 'centre' ba. Sai aka kai mu unguwar Dankali wajen wani dan uwa. A can muka kwana. Da safe na sake dawowa 'centre'. A nan ne nake jin labarin abin da ke faruwa a Gyallesu. An harbe ni ranar Asabar da rana, to har ranar Alhamis ba a yimani aiki ba. Kuma ban sha kwayar magani ko daya ba. To, a ranar ce wasu'yan'uwa suka ce tunda gari ba lafiya, kuma babu'yan ISMA, a san yadda za a yi ko da allurar tetanus a yi mani. In kuma bar garin in je wani garin don a yi mani aiki. To, duk da haka ban dauki wani mataki ba. Sai muka ji cewa Sojojin sun fara bi gida-gida suna neman 'yan'uwa Suna harbe su. Hakan ya sanya 'yan'uwa suka ce dole ne in bar Zariya zuwa wani garin domin a yimani aiki. Suka bani Kudi, na kama hanya na zo Gusau. A kan hanyar Gusau, na dinga haduwa da shingayen sojoji. A randar Kano, na ga Wasu sojoji sun zo sun harbe wasu 'yan'uwa. Bayan na wuce Giwa, na ga wani shingen sojoji. Sa'annan bayan na wuce Marabar Yakawada nan ma sun sa shinge. Haka kuma a gaban Tsafe sun sa shinge. Su har ma da tankar yaki. da" yaki. Saina karasa Gusau. lna zuwa sai na nemi lambar Sirajo Kwamandan Harisawa. Shi ne ya ba ni lambar Amir din yan'uwa na Gusau. To, a nan ne aka yi mani aiki. Ka dai ji yadda wannan waki'a ta faru da ni. Fatata Allah ya kare yadda mana Sayyid (H) tare da sauran yan'uwan da ke tsare, ya kwato mana su, ya karbi shahadar wadanda suka yi shahada.
Ilahee yarabbal Alamin.
0 Comments