Kamar yadda aka saba a duk shekara 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) , na gudanar da taro na musamman domin tunawa da waki'ar Kudus da ta auku a ranar 25 ga watan Yulin shekarar 2014, inda sojoji suka aukawa masu muzaharar Kudus a garin Zariya ta jihar Kaduna inda suka kashe 'yan'uwa 34 ciki harda 'ya'yan Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky guda uku; Shahid Ahmad, Hamid da Mahmud Zakzaky. Tare da raunata da dama ciki harda Sayyid Ali Ibraheem Zakzaky.
Taron na bana shi ne karo na Takwas, kuma ya gudana ne a muhallin Shahidai na Darur Rahma dake kauyen Dembo a Zariya.
An fara taron na yau ne da misalin karfe 7:30 na safe. Inda kamar yadda yake a al'ada aka bude taron da addu'a da kuma karatun Alkur'ani mai girma. Bayan nan an bai wa mawaka dama suka haskake wurin da wakokin munasabar ta yau. Daga bisani, bangarorin Kashafa da Jasaz da sauran su, suka gabatar da 'Display' dangane da Munasabar.
An saurari Jawabin Sayyid Ibrahim Zakzaky Wanda yayi jiya yayin ganawa da iyalan Shahidai da Yayi a gidan sa dake Abuja bayan nan Kuma aka Gabatar da Wanda suka ga waqi'ar da idonsu. Sukayi jawabai Bayan kammala jawabansu, an kai ziyara ga kaburburan Shahidan na Kudus. A karshe kuma aka raba kyautuka ga Iyalan Shahidan, sannan aka karkare da addu'a da misalin karfe 10 da mintoci
Idan mai karatu bai manta ba, waki'ar ta auku ne a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, wanda Kanal S. Okuh ya jagoranci kashe 'yan'uwa Musulmi a yayin muzaharar.
Al'umma daban-daban na cikin gida da waje sun yi Allah-wadai da wannan aika-aikar. Haka zalika kungiyoyi na duniya mabambanta na kare hakkin bil'adama da na Musulunci sun yi Allah-wadai da gwamnatin Jonathan bisa wannan aika-aikar.
Haka ma fitattaun al'umma daga masu rajin kare hakkin bil'adama, 'yan jarida, 'yan siyasa, Malaman addini, Jami'an Diflomasiy
0 Comments