Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi jawabin ne a gaban ba’adin wakilan yan uwa na bangarorin Harka a ranar Lahadi 18 ga Zulhijja 1443 (17/7/2022) a gidansa da ke Abuja.
GODIYA GA ALLAH
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala wa Barakatuhu.
To, da farko zan fara da taya mu murna da cewa, muna godiya ga Allah Ta’ala wanda ya sanya mu cikin wadanda suke cikawa da alkawarin da ya mana na waliccin Amirulmuminin da A’imma (AS). Wannan ba karamar ni’ima bace.
Kuma muna godiya ga Allah Ta’ala da ya karramamu da wannan rana wacce a ciki ya dauki alkawarin al’umma ga wilayar wanda ya walittar, wilayar Amirulmuminin da ‘ya’yansa Ma’asumai (AS).
To kuma muna godiya ga Allah da ya sanya cikan addininsa da kammalar ni’imarsa da wilayar Amirulmuminin Ali Bin Abidalib (AS).
ALLAH TA’ALA YA YI MANA BABBAN NI’IMA
To ni’ima Allah ya mana bayan ni’ima, na farko ni’imar samar da mu daga rashi, da babu mu, kuma Allah Ta’ala ke halitta, shi ya ga dama ya haliccemu (daga rashi), to kuma bayan halittar kuma yana iya yinmu a wasu halittu daban tunda gashi da halittu daban-daban; ga wasu masu tafiya a cikinsu, wasu masu kafafu hudu, wasu suna iwo a ruwa, wasu suna tashi a sama, gasu nan dai, duk halittunsa ne, duk wanda ya ga dama yana iya yinmu yadda ya ga dama, amma sai ya zabi ya yi mu a matsayin mutane, wadanda ya fifita su birbishin abubuwa da dama da ya halitta.
Domin ana cewa tsakanin Mala’iku da mutane su waye suka fi? An tambayi Amirulmuminin (AS). Sai yace shi Mala’iki ruhi ne tsattsarka, an saka masa hankali amma bai da sha’awa, ita kuma dabba an saka mata sha’awa ba hankali, shi kuma mutum sai aka gwama masa biyun, saboda haka idan mutum hankalinsa ya fi karfin sha’awarsa to ya fi Mala’ika, idan kuma sha’awarsa ta fi karfin hankalinsa to dabba kuma ta fi shi.
Allah Ta’ala yana cewa: “Laqal khalaqnal insana fi ahsani taqweem, summa radadnahu asfalas safilin.” (Suratul Tin: 4-5). Shi Mutum kenan. Na farko dai an bashi babban dama, an fifita shi, in ka ga ya kaskanta shi ya kaskanta kansa.
Sannan kuma a cikin mutane wadanda ya fifita (halittarsu), sai kuma Allah Ta’ala ya kara mana wani fifikon, shine fifikon kasancewa Musulmi, wanda mafi yawan mutane su kuma ba Musulmin bane. Fifikon Imani. Wannan daraja ce bayan daraja.
Sai kuma Allah ya kara mana wani fifiko a birbishin kasantuwarmu Muminai, shine sai ya saka mu cikin yan al’ummar Manzon Rahma (S) wacce ita ce fiyayyiyar al’umma. “Khairu ummatin ukhrijat linnasi.” Sai ya saka mu a cikin wannan al’umma din. Kai! Wannan ni’ima bayan ni’ima Malam.
To, cikin ‘yan al’ummar Annabi din kuma, sai Allah ya kara mana wani karin fifiko, ya saka mu cikin Ahalin Wilaya.
To kowacce ni’ima sai ka ga ta fi wacce take kafinta, domin ni’imar mutum ya zama Ahlul Wulaya shine birbishin ya zama Musulmi, saboda kebancewar kebancewa ne.
To kuma baya ga zama Ma’abota Wilaya din, ka san wasu mutane basu da ‘ragaba’ da addini? Sai ka ga cewa mutum gashi dai ya yi sa’a an haife shi Musulmi, kuma tana iya yiwuwa ma yana sallah yana ba da zakkah, amma dai shi inda za a ce yanzu ya kamata al’umma ta zauna ba a turban addini ba? Sai ya yi maka garau. Yace an hana ka sallah ne? shi a ganinsa ba lalai ne a yi wannan (yunkurin dawo da addinin ba). To, sai Allah ya saka mu Ahalin wadanda muka ce ba kawai mun yi imani bane, a koma ga abin da muka yi imani a kai din. Al’ummar da muka samu kanmu ta koma ga wannan.
To wannan kuma ba karamin aiki bane, wanda yake a saka ka a cikin ‘mutaharrikeen’, ka zama ‘mutaharrik’ shima babban ni’ima ne. Domin Allah Ta’ala yana cewa “Waltakun minkum ummatun yad’una ilal khairi wa yu’umuruna bil ma’arufi wa yanhauna anil munkari….” (Ali Imran: 104). Daga cikinku ku muminai kenan, a samu wadanda za su yi umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna. Ya zama su suna cewa ga abu mai kyau a yi, wanda bai dace ba a bari.
Wato ina fadin ni’imomi ne bayan ni’imomi, wanda yake “Wa’in ta’uddu ni’imatallahi la tuhsuha…” (Nahli: 18). To Alhamdulillahi, mun godewa Allah da ya mana wadannan ni’imomi.
BA DA UZURI
Wannan rana ta musamman, na san yanzu kuma bayan na taya ku murna dole na kuma baku hakuri, domin daidai wannan lokacin ya kamata mutum ya zama kila yana gida ne, saboda ko ba komai ana son a yi azumi ranar Ghadeer, kuma mu a wajenmu tafiyar da ta sabbaba yin Kasaru ta yanke azumi, saboda haka ba mu gwamawa, amma dai ladan na nan insha Allah. Ko mutum bai yi ba yana da ladan, tunda yake daman ‘ihtimalan’ in yana zaune a gida ne zai yi ne.
Kuma dama mun saba mu kan yi bikin Ghadeer a Zariya, kuma duk yan uwa su kan hallara, sai bayan mun gama ne su kan je su yi a nasu garuruwan. Har na dan duba wanda aka yi na karshe kafin waki’a sai na ga mun dauki kwanaki ne muna yi a jere. Sai ya zama Tafsirin da muka yi ranar Laraba kafin Ghadeer din kamar ma dai Ghadeer din ne, don muna fassarar wata aya ce a cikin Suratul Ali Imrana wacce ta yi magana dangane da al’amarin Uhud da abin da ya faru, aya ta sauka dangane da wadanda suka gudu da kuma wadanda suka dake. Sai ya zama duk maganar a cikin sharhin ma sai Hudubobin Ghadeer suka fito. Har nace to mun ma fara Ghadeer. To kuma muka yi Ghadeer din kwanaki a jere, Juma’a, Asabar, Lahadi da Litini, a jere kwana hudu muka jera muna Ghadeer.
To wannan al’amari yanzu tunda mun samu wata jarabawa. Allah ya jarabcemu da wadansu mutane da aka basu jinga na wani aiki, kuma suka ga su za su yi wannan aikin, duk da Allah ya gwale su amma dai sun yi barna iya iyawarsu. Na san cewa mun yi magana kafin waki’a cewa in ma sun yi sai dai su karfafa al’amarin insha Allahu. Kuma abin da ya farun kenan.
To shikenan, yanzu ya zama bisa lalura ya zama dole in ma za mu yi batun Ghadeer yanzu a takure za mu yi tunda ‘qalilan’ din mutane muka gayyato muka ce to a dan zo nan ko da a gaggaisa a lokacin Ghadeer din kawai, amma dai Ghadeer na sosai wanda muka saba yin bikin kwana da kwanaki ba za mu iya yi ba.
Amma yanzu haka ana yi a Maraba. Kuma dama lokacin Layya akwai wata Saniya cikin wanda muke kiwo, aka nemi wanda yake rike da saniyar ba a same shi ba a lokacin, sai aka ce to a bari a yanka da Ghadeer. To kuma cikin ikon Allah dama akwai wani rakumi shima da aka kawo shi da nufin a soke lokacin Mauludin Sayyida Zahra (SA) amma shima sai ya zo a makare, shima sai muka ce a yi a wani munasabar, muka ce za mu yanka a wannan lokacin. Sai kuma ikon Allah aka aiko mana da karin shanu har da karin rakumi ma. Saboda haka yanzu haka rakuma ne da shanu da rago, duk an samu an yayyanka su. Don haka ta wannan bangaren Alhamdulillah. Muna fatan ya zama za mu soki rakuma da yawan gaske.
RANAR GHADEER BABBAN IDI NE
To ranar Ghadeer babban Idi ne, wanda aka ce babu wani Annabi da Allah ya aiko face ya yi idi da wannan Idin. Kuma Idi ne a kasa, Idi ne a sama. Wannan ba bisa hadari bane. Ba bisa hadari bane ya zama cewa rannan ne ake kafa ‘Ausiya’.
Rannan Annabi Adamu (AS) ya kafa wasiyinsa Shi’is. Rannan ne Ibraheem (AS) ya kafa wasiyinsa. Haka ma rannan ne Musa (AS) ya kafa Wasiyinsa. Haka ma rannan ne Isa (AS) ya kafa wasiyinsa. To ka ga ba zai yiwu ya zama hadari ba kuma ya zama rannan ne kuma wannan Manzon (S) ya kafa nasa. Me yasa ya zama wannan ranar ce ake ta kafa ‘Ausiya’?
Kuma rannan ne Allah Ta’ala ya tsamar da Ibraheem (AS) daga wutar Namaruzu. Ka san makiya sai suka malkwaya suka ce wai ranar Ashura ne. Muka ce to mun san dalilin da ya sa dole ku juya, saboda kun san wannan ranar, kun san darajarta. Saboda haka sai kuka juya kuka ce ranar da aka kashe Imam Husaini (AS) ce ranar da ta fi daraja. Sai dai basu da karfin halin su ce babbar darajar wanna ranar shine kashe Imam Husaini (AS). Basu da wannan karfin halin. Sai suka yi shiru dangane da wannan, suka kirkiro abubuwa da dama, alkairan duniya duk gaba daya suka ce ranar Ashura ne.
Suka ce rannan ne Allah ya karbi tuban Adamu, rannan ne ya saukar da shi doron kasa, rannan ne aka tsamar da Nuhu daga ruwan dufana, rannan ne aka tsamar da Ibraheem daga wutan Namarud, rannan ne aka shallake da Musa (AS) da jama’arsa daga kogi aka halaka fir’auna, rannan ne aka yi kaza, har ma wani ya bugi kirji yace wai rannan ne aka haifi Annabi (S). Akwai wanda ya bugi kirji ya fada, yace rannan ne ma aka haifi Annabi (S). Saboda mene? Suna kaucewa ranaku da suka sani saboda gudun (darajtata), don sun san wannan rana ta nasabci rannan abubuwa da dama sun auku.
To rannan ne kuma ba bisa hadari ba Manzon Allah (S) ya nasabta wasiyinsa. Ka ga ba bisa hadari bane.
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
0 Comments