Tasirin Tsayuwar Su Sayyid Ahmad Zakzaky Ga Rayuwar Matasan Harkar Musulumci A Najeriya.–Ibrahim Azzamfarawy


Wato ba zaka san Girma, Matsayi, da Muhimmancin da Shahid Sayyid  Ahmad ya kawo a rayuwar Matasan Harka Islamiyya bah, se kayi dubi ga rayuwar Matasan sauran Al'umma.

Zaka ga mafi yawan su ba ruhin Addini a tattare dasu, ballantana ruhin kawo sauyi a cikin Al'umma. Mafi yawa sun shagala ne da kyale kyalin rayuwa, burin su daya ne; su girma, su samu kudi, su auri mace me kyau, su mallaki gida me kyau da mota me kyau...

Se ya zamana su ma Matasan Harka hakan yana tasiri a kansu, mafi yawa kawai an haife su a Harka Islamiyya ne, amma basu san Hadafinta ba, basu san ina aka fito ba, ina ake kai, da kuma ina za a je..

A wannan yanayin Shahid Sayyid Ahmad ya mike shi da Mataimakan sa Yan'uwan sa (Shahid Sayyid Hamid da Shahid Sayyid Mahmud) domin kawo sauyi a rayuwar Matasan mu, da kwakkwafa tunaninsu, tare da kore masu tunanin "Dan buraza" ko "Yar Buraza".
Zuwa ga "Buraza" da "Sista".

Wato su ji cewa su ma Yan Harka ne wadanda zasu ba da Gudummuwa kamar yadda Iyayensu suke badawa ko ma fiye da haka...

To dama dole se an fuskanci Yan "hana ruwa gudu" a kowanne Al'amari na Allah, a hakan dai Shahid ya cigaba da wannan gagarumin aiki duk da cewa sakon ya gagara isa ga dukkanin Matasa kamar yadda yake buri...

Sai ga 25 july 2014 ta zo; Bakar Rana, Ranar Bakin ciki da Juyayi, Ranar da Harka tayi rashin Gwaraza Hazikai..
Ranar Shahadar su Sayyid Ahmad, da Yanuwa 30..

Se dai duk da wannan rashi da akayi, akwai wata Natija gagaruma da hakan ya samar, shine; 
FARKAWAR KASO MAI YAWA NA MATASA.. 
A lokacin ne muka fahimci wannan hadafi na Yaya Ahmad, muka rungume shi hannu bibbiyu, kuma mukayi alkawarin tallafa ma Jagoran sa, kuma Jagoran mu, domin kai wa ga gaci (Kamar yadda yake burin Shahid din).

Wannan babbar alama ce ta tasirin da jinin Shahidi yake dashi a cikin Al'umma...

A kullum Addu'ar mu ita ce;
Allahu ya tabbatar damu a tafarkin da su Shahid Ahmad suka tabbatu akai har suka riski Babban Rabo. Allahu ya sa mu zamo kayan aiki wurin Jagora (H) kamar yadda su Shahid suka kasance...


Assalamu Alaikum Ya Shuhada!

#25JulyNeverForget

–Ibrahim Azzamfarawy
26/12/1443
25/07/2022

©Freedom Fighters NG.

Post a Comment

0 Comments