Nasarar Yan gwagwarmaya A Shekara ta 2000 Ya kawo Karshen Kafa Fadaddiyar Isra’ila


Nasarar Yan gwagwarmaya A Shekara ta 2000 Ya kawo Karshen Kafa Fadaddiyar Isra’ila

Babban sakatare Janar din kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan nasrullah da yake bayani game da cika shekaru 40 da kafa kungiyar ya fadi cewa gagarumar nasarar da yan gwagwarmaya suka samu kan Isra’ila a yakin shekara ta 2000 shi ne ya kawo karshen mafarkin isara’ila na kafa Fadaddiyar Isra’ila

Har ilayau sayyid Nasrulla ya fadi cewa daya daga cikin sakamakon da aka samu na tsayin Dakar yan gwagwarmaya a yakin watan yulin shekara ta 2006 shi ne rushe mafarkin kafa sabuwar gabas ta tsakiya, da kuma kawo karshen shirin kafa fadaddiyar isra’ila , ko da ba’a ce komai game da rawar da suka taka wajen tabbatar da hakkin labanon a bangaren man fetur da iskar gas.

Ya kara da cewa cin nasarar da hizbullah ta yi a yakin kwanaki 33 yana daga cikin manayan nasarorin da kungiyar ta samu a tarihinta. Yace hizbullah tana adawa da kulla hulda da isra’ila kuma za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga alummat falasdinu

Daga karshe nasarullah ya fadi cewa hizbullah ta ci gaba da rike dangantaka ta kud-da-kud tsakaninta da dukkan kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu kuma za ta ci gaba da yin haka, ya jaddada cewa lamarin falasdinu wani bangare ne na Addini , al’adu mutunci da martabar Alummar kasar kuma ba’za a iya yin watsi da hakan ba ta kowanne hali.


Source: HausaTv

Post a Comment

0 Comments