Takaitaccen Tarihin Nelson Mandela (1918-2013)

An haifi Nelson Rohlihlahla Mandela ne a ranar 18 ga watan Yulin 1918 a kauyen Mvezo na yankin Umtata wanda a lokacin yake lardin Cape na kasar Afirka ta kudu. Asalin sunan da mahaifinsa ya nada masa shi ne ‘Rolihlahla’ wanda a yaren kabilarsa ta Xhosa yana nufin ‘mai kiriniya’ ko ‘neman fitina’ wanda kuma daga baya lalle sunan ya bi shi saboda irin kiriniyar da aka ce yana da shi tun yana karami sannan kuma ya ci gaba da binsa wanda ana ganin yana daga cikin abubuwan da suka sanya shi shiga kungiyoyin fafutuka tun yana karami. Iyayensa dai su ne sarakunan kabilar ta su.

Iyayensa dai ba wasu masu abin hannu ba ne sannan kuma ba su ma yi karatu ba, don haka Nelson Mandela ya fara rayuwarsa ne a wani kauye da ake kira Qunu inda a nan yake tafiya kiwon dabbobi tare da sauran abokansa. Don haka ya yi mafi yawan rayuwarsa ne a jeji. Sai dai kuma daga baya mahaifiyarsa ta sanya shi a wata makaranta ta ‘yan Mission ganin cewa iyayen nasa masu riko ne da addinin Kirista hakan kuwa ta faru ne tun yana shekaru bakwai a duniya. A wannan makarantar ce dai daya daga cikin malaman makarantar ta sanya masa sunan Nelson wanda suna ne na turawa, a lokacin yana da kimanin shekaru 9 a duniya. Shi kansa Mr. Mandelan ya ce bai san dalilin da ta sanya masa wannan sunan ba. Har ila yau kuma a daidai wannan lokacin ne mahaifinsa ya rasu saboda cutar da yake fama da ita. Don haka daga nan ne mahaifiyarsa ta dauke shi da mika shi wa sarkin garin nasu don ci gaba da kula da shi. Sarkin dai ya kula da shi tamkar dansa lamarin da ya ba shi damar ci gaba da karatu a wata makaranta ta ‘yan Mission dake jikin fadar sarkin inda a nan ne ya koyi turanci da sauran ilmummuka daban-daban na lokacin musamman tarihi, wanda aka ce ya taimaka masa kwarai da gaske wajen gina wannan akida tasa da Afirkanci da kaunar kasarsa bugu da kari kan kyamar irin mulkin mallakan da turawa suke yi.

Daga nan ne kuma a wajen kimanin shekarar 1936 Nelson Mandela ya fara karatun sakandarensa a wata makaranta ta kwana mai suna Clarkebury Boarding Institute, wacce duk da cewa makaranta ce da ake karantarwa irin ta turawa amma dai mafi yawan daliban wajen bakaken fata ne na Afirka. Daga baya kuma ya bar  wannan makarantar inda  ya koma wata makarantar ta daban wacce mafi yawa daga cikin ‘ya’yan sarakuna da dagattan yankin ne suke karatu a wajen. Duk da cewa a wajen an fi fifita irin al’adu na turawa to amma shi Mandela irin ala’dunsu na bakaken fata da kabilun  wajen ya fi burge shi. Kamar yadda kuma a lokacin daya daga cikin malaman makaranta shi ma ya karfafa shi kan hakan. Don haka ana iya cewa wannan makarantar ma ta taka gagarumar rawa wajen kara karfafa akidar kishin kasa a cikin zuciyar Mandela.

Bayan nan kuma ya ci gaba da karatunsa na neman digiri na farko a Jami’ar Fort Hare inda a nan ne ma ya hadu da wasu daga cikin abokansa irin Oliver Tambo da K.D. matanzima wadanda daga baya suka zamanto abokansa cikin gwagwarmayar da ya dinga yi da akidar nuna wariyar launin fata. Sai dai kuma bai gama karantunsa a wannan makarantar ba saboda korarsa da aka yi sakamakon ruwa da tsaki da ya yi cikin wani bore da dalibai suka yi dangane da irin abincin da ake ba su a makarantar.

Shekarun 1941-1943 sun kasance daga cikin shekarun da suke da tasiri a cikin rayuwar Nelson Mandela don kuwa a wadannan shekarun ne ya dawo birnin Johannesburg inda a nan ne ya fara aikin gwamnati, sannan kuma a lokacin ne ya fara aurensa na farko da kuma kasantuwa tare da ‘yan jam’iyyar ANC mai fafutuka sannan kuma ya ci gaba da karatunsa. Kamar yadda kuma a lokacin ne ya fara shiga harkoki na siyasa da kuma aikin lauya da yake yi a wannan bangaren.

A shekarar 1944 ne marigayi Mandela ya yi aurensa na farko inda ya auri Madam Evelyn Mase wacce ita ma wata ‘yar fafutuka a jam’iyyar ANC din wanda kuma suna sami haihuwa a tsakaninsu.

Don haka ana iya cewa tun yana dalibi, Nelson Mandela ya kutsa tsundum cikin harkokin na siyasa da gwagwarmaya inda tun yana saurayi ya fara jagorantar zanga-zangar nuna rashin amincewa da salon mulkin nuna wariya dake gudana a kasar, kuma haka ya ci gaba da irin wadannan ayyukan na sa na fada da wariyar launin fata tare da abokansa a fili har zuwa lokacin da aka haramta jam’iyyar ANC din.

A wannan lokacin dai Mandela da wasu daga cikin na kurskusa da shi sun kai ga shawarar cewa lalle ya zama wajibi a dau makami wajen kwato hakkokin bakaken fata na kasar.

Don haka ne daga nan ya fara tunanin hanyoyin da za su fara samo makamai musamman daga kasashen waje musamman kasar China a lokacin.

Bayan fitowar wannan kokari na su ne da kuma wasu ayyuka da suke yi ya sanya gwamnatin lokacin a ranar 5 ga watan Disamba 1956 ta kama Mandela tare da wasu manyan kusoshin ANC din inda aka tsare su na wani lokaci bisa cajin cin amanar kasa. An ci gaba da tsare su har zuwa ranar 9 ga watan Janairun 1957 lokacin da aka ba da belinsu. Sai dai kuma an sake kama su da ci gaba da tsare su har dai zuwa shekarar 1961 lokacin da alkalin da ke musu shari’a ya sake su saboda rashin dalilin da ke tabbatar da laifin da ake zarginsu da shi.

Mandela ya ci gaba da wannan gwagwarmaya tasa da gudanar da tarurruka na sirri a ciki da wajen kasar tare da wasu shugabanni ‘yan gwagwarmaya har zuwa shekarar 1962 lokacin da ya fita kasar a asirce don nemo taimako na kudade da kuma makamai daga waje da kuma ba da horo da dabarun yaki ga ‘yan jam’iyyar ta su ta ANC. Bayan dawowarsa ne jami’an tsaro suka kama shi da kuma tsare shi. Daga baya dai an gurfanar da shi da wasu abokansa a gaban kotu da zargin zagon kasa da kokarin kifar da gwamnati da sauransu. Daga karshe dai bayan doguwar shari’a kotun ta sami Mandela da wasu abokansa biyu da laifi inda aka daure su rai da rai a gidan yari maimakon hukumcin kisan da masu shigar da kara suka bukata. A nan ne aka tsare su a gidan yarin Robben Island dake Pretoria inda suka shafe shekaru 18 a wannan gidan yarin cikin mawuyacin hali. Daga nan kuma daga shekarar 1982-88 an mayar da Mandela zuwa gidan yarin Pollsmoor da ke birnin Cape Town sannan daga baya kuma aka mai da shi wani gidan yarin na daban na Victor Verster inda a nan ne ya ci gaba da zama har lokacin da aka sake shi a shekara ta 1990.

A wannan gidan yarin ne aka ci gaba da gudanar da tattaunawa tsakanin Mandela da masu mulki lamarin da ya kai ga sako shi a ranar 11 ga watan Fabrairun 1990.

Bayan fitowarsa dai an ta gudanar da tattaunawa don kawo karshen mulkin wariya a kasar ta Afirka ta kudu wanda aka kawo karshensa da gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 1994 inda Mandela ya lashe zaben inda aka rantsar da shi a ranar 10 ga watan Mayun 1994 a matsayin sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu sannan kuma bakin fata na farko da ya taba rike wannan mukamin.

Shugaba Mandela ya rike wannan mukami ne har zuwa shekarar 1999 lokacin da ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan kin amincewa da ya yi na ci gaba da mulkin duk kuwa da yakinin da ake da shin a cewa idan da ya tsaya da ya lashe. Bayan saukarsa daga mulki dai marigayi Mandela ya ci gaba da gudanar da ayyuka na agaji da fada da cututtuka musamman cutar nan ta AIDS.

Bayan matarsa ta farko shugaba Mandela ya sake yin aure inda ya auri Winnie Mandela wacce suka sami haihuwa a tsakani amma daga baya dai bayan fitowarsa daga gidan yari sun rabu saboda faruwar wasu abubuwa da ba su yi wa mandelan dadi ba a lokacin da yake tsare.

Daga baya kuma ya auri tsohuwar matar tsohon shugaban kasar Mozambique Samora Mashel wato Graca Machel.

Tsawo rayuwarsa dai Mr. mandela ya zamanto mutum ne da ake girmama shi da duk duniya saboda irin rashin dakan da ya yi wajen samar wa wal’ummarsa ‘yanci da kuma dattukan da ya nuna bayan fitowarsa da kuma zama shugaban kasa.

Allah ya yi masa rasuwa ne a ranar 5 ga watan Disamban 2013 yana da shekaru 95 a duniya.

Post a Comment

0 Comments