Daniel Pom, DPO na Soba da ya Jagoranci kisan 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na garin Soba dake jihar Kaduna a yayin muzaharar Ashura ta 1444 fargaba, razana da tsoro ta sanya an sauya masa wurin aiki, inda aka mayar da shi karamar Hukumar Chikun.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa tun a shekaranjiya aka yi masa tiransifa daga Soba zuwa karamar hukumar Chikun.
Tun bayan jagorantar kisan da ya yi na ba gaira ba dalili, Daniel Pom DPOn na 'yan sanda ya shiga 6uya, ya daina kwana a gidansa saboda tsoro da fargaba.
Sai dai 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun labarta mana cewa ba za su ta6a yafewa DPO din ba. Kuma dole za su dauki matakan da suka dace akansa duk inda kuwa za a maida shi a fadin duniyarnan.
©Ammar M. Rajab
0 Comments