Sunana Ummulkhairi Salisu. Ina zaune ne a Karamar Hukumar Isa a jihar Sakkwato. Shekaruna 14. Ina karatu ne a Soba Fudiyya Secondary School. Ranar Asabar tun da wuri muka shirya zuwa Zariya, daman ranar akwai bikin sa tuta a Husainiyya Bakiyyatullah. Lokacin da muka shigo Zariya kai tsaye sai muka nufi Husainiyya din. Kafin mu karasa wajen, sai aka sanar mana cewa Sojoji sun zo Husainiyya sun yi harbe-harbe, yanzu haka ma sun kewaye ta sun kuma killace hanyoyi ba damar wucewa. Sai muka juya muka tafi Gyallesu gidan Malam. Muna nan Gyallesu har zuwa karfe 9:00 na dare ba wani abu, wasu a cikin mu har sun kwanta barci. Misalin karfe 10:30 na dare sai muka ji ana kabbara, ana cewa a fito Sojojí sun shigo Gyallesu. Muna ta jin karan harbi, sai aka ce sun kara matsowa suna so ne su shigo gidan Sayyid, su 'yan'uwa sun fahimci manufarsu. Don haka sai aka dinga kabbara, dama su kuma sun zo da shiri sosai, sai suka dinga harbi suna kashe 'yan'uwa, mu a lokacin sai aka saka mu wani waje aka ce mu tsaya nan kada mu je ko'ina, muna nan har safiya ta yi Sojoji na harbin 'yan'uwa. Duk da an ce mana mu tsaya kada mu aga ko'ina, amma dole yanayin harbin da Sojojin ke yi ba kakkautawa ya sa dole muka nemi wani wajen daban.
Ranar Lahadin ne da safe muka ji labarin cewa Sojoji sun harbi Malam Turi har ma ya yi shahada. To, a nan inda muke, sai muka ga Sojojin sun shigo sun harbe duk wadanda muke tare da su. Allah ya yi a lokacin ba su harbe ni ba suka fita. Da suka fita sai wasu 'yan'uwa suka shigo aka fita da mu, ni da wasu aka kai mu gidan Harisawa aka ba mu aiki. A nan kofar gidan Harisawa Sojoji suka harbi wata Sista, sai muka riko ta muka shigo da ita cikin gida, daidai lokacin su kuma Sojojin sun matso suna son su shigo gidan Malam, su kuma Burazu da suka fahimci haka suka fuskance su, a wannan lokacin, tun ana daukar 'yan'uwa wadanda aka harba har aka daina, saboda sun yi yawa. A cikin gidan Harisawa sai muka shiga wani daki muka rufe. Muna ciki, sai muka ji zafi ya yi yawa, ko da muka taba jikin ginin sai muka ji zafi sosai, da muka duba ashe an sa wuta ne a dakin ba mu sani ba. Ko da muka fito ashe gidan ya kama da wuta, ragowar 'yan'uwa da ke wurin sai aka dinga shiga ana dauko masu rauni wadanda ba sa iya tafiya ana fita da su waje. Dole aka baro gawawwakin 'yan'uwa cikin dakin domin ga su da yawa, kuma ba yadda za a yi da su; dole aka bar su ciki dakin suka kone, sauran ragowar dakuna uku na gidan suka kama da wuta.
Muna nan sai ga Sojoji sun shigo suka kama harbin 'yan'uwa, sai wasu Sojojin suka ce mana mu tashi mu fita waje, to lokacin duk wanda ya tashi in zai fita sai su harbe shi, sai ni na ki fita. Ni dai ina ganin da in zo fita su harbe ni gara su harbe ni a inda nake. Sai wani Soja ya lura da ni, ya kira ni ya ce in tashi in fita, sai na kyale ban ce masa komai ba. Shi ne sai ya daga bindiga ya harbe ni. Bayan ya harbe ni ina kwance, sai wani Haris da Allah ya kiyaye ba su harbe shi ba, ya hango ni sai ya ce in tashi na ce masa ba zan iya ba, sai ya karaso ya taimake ni ya fita da ni waje, don gidan wuta ta kama sosai har ma wata Sista da aka harba gashin kanta ya fara konewa. A nan wajen da aka kawo ni mun tarar sojoji sun tara wasu Sistoci da Burazu da aka harba suka bar mu nan jininmu na ta tsiyaya a kasa. Muka ce da Sojojin su taimaka su kai mu Asibiti, suka ce sai Ogansu ya zo. A gaskiya Sojojin sun nuna rashin tausayi, ga mu da rauni na harbi, amma suna ta dukan mu. Ba su kai mu Asibiti ba, sai dai kawai sun kwashe mu suka wuce da mu bariki. A can din ma sun sa an wanke mana wurin da jini yake zuba ne. Kwananmu biyu a wurinsu. Muna nan sai muka ga an shigo da Yaya Suhaila da Sajida, sai dai a nan muka bar su, sai suka wuce da mu Asibitin Shika. Ranar farko da suka je damu sun ba mu, amma rana ta biyu da za su kai mu Asibiti ba su ba mu komai ba. A bariki ba su yi mana komai ba, amma lokacin da suka kwaso mu a mota daga gidan Harisawa sun doki 'yan'uwa sosai, har ma wani dan uwa ya yi shahada, kuma a can bariki din sun yi mana maganganu na izgili, har wasu a cikin su na cewa mu tuba mu bar Shi'ah, wai muna bata lokacinmu ne kawai da dai sauran maganganun wauta da jahilci. Sun harbe ni ne a kafa, kuma harsashi biyu ne aka cire a jikina.
Gaskiya a lokacin ba wai ina tunanin halin da nake ciki ba ne, ina tunanin halin da Abba (Shaikh Zakzaky) ke ciki ne. Mun baro wadannan azzaluman can, kuma har sun sa wuta a gidan, ba mu san abin da zai biyo baya ba. Sannan a nan bariki mun baro Yaya Suhaila da Sajida a hannun Sojoji, suna iya kashe su tunda daman kisan kai ne suka fito yi. Wannan shi ne tunanina a lokacin. Wannan Harka ba zancen tsoro ko batun razana. Wannan abin da suka yi mana don su tsorata mu, sun dada karfafa mu ne. Wannan Harka hanyar tsirar mu ce, sai dai kawai mu nemi sabati s wajen Allah. Kirana daya ne, shi ne gwamnati ta sako mana Jagoranmu, su kuma sako mana 'yan'uwanmu da suke tsare, har ila yau su ba mu gawawwakin 'yan'uwanmu da suka kashe.
0 Comments