Ranar 20 ga Safar wacce aka fi sani da Ranar Arbaeen, Kamar yadda take alamta kwanaki 40 da shahadar Imam Hussain (AS), a Karbala. Tun bayan faduwar Saddam Hussain (LA) na Iraqi a shekarar 2003, duniya ta cigaba da ganin miliyoyin mutane wanda suke zuwa Iraqi domin tunawa da ranar Arbaeen ta hanyar yin tafiya daga Najaf zuwa Karbala a cikin wasu yan kwanaki kalilan. Wasu zasu yi ta tunanin menene Arbaeen kuma menene Anfanin Arbaeen a Addinance?
Ziyarar Arbaeen na Imam Hussain ta samo asali a shekara ta 61 bayan hijira, lokacin da sahabin Mamzon Allah Jabir bn Abdullah al-ansary ya iso Karbala a ranar 20 ga watan Safar, ya tarar da Kaburburan (Jam'in Kabari) Imam Hussain (AS) da sahabban sa a filin Karbala.
Wata ruwayar da ruwaito cewa, Tawagar Imam Hussain (AS) wadanda Yazidu (LA) gake tsare dasu a Damascus (Syria a yanzu), suna kan hanyar su ta zuwa Madina bayan an sake su. A cikin tafiyar, sun iso Karbala a ranar 20 ga watan Safar kuma suka hadu da Jabir. Bayan sun baiwa Jabir labarin yadda waqi'ar Karbala ta faru a ranar Ashura, sai suka shiga karanta ziyara (Addua), da yin zaman makokin Shahidan.
Daya daga cikin al'amuran Arbaeen mafi shahara shine Hadisin Imam Hassan Al-askry (AS), wanda a ciki yake cewa: "Alamar mumimi guda 5 ne; Sallah rakava 51 a rana, Ziyartul Arbaeen, Sanya zobe a hannun dama, Yim sujuda (Sujud-ul-Shukr), da kuma karanta Basmala da babbar murya a cikin Sallah".
Haka zalika, a wata ruwaya Imam Sadiq (AS), yake cewa daya daga cikin sahabban sa ya ziyarci Imam Hussain (AS) a ranar Arbaeen da shahadar sa, yana mai nuni da irin mustahabbancin ziyarar Imam a wannan rana ta musamman. Wanda shi ke nuna cewa, Ziyarar imam Hussain (AS) a ranar Arbaeen ba an kirkire ta bane, aa, tana daga cikin koyarwar Manzo (SAW) da kuma koyarwar magada iliminsa, Imaman Ahlulbayt (Alaihimus-Salam).
A wasu ruwayoyin, Ziyar Arbaeen tana da matukar muhimmamci da kuma dimbin lada. A wata ruwaya Imam Sadiq (AS) yake cewa: "Duk wanda ya tafi zuwa kabarin Imam Hussain AS (mavana yayi tattaki), Allah zai rubuta masa lada 1000 a kowane taku, sannan ya goge masu zunibi 1000, ya kuma daga darajar zuwa 1000".
A lokacin mulkin zalunci na Saddam Hussein, an sanya takunkumi akan wannan tafiya, amma tun bayan faduwarsa, Iraki ta ga farfadowar wannan tafiya, wanda aka danne shekaru da yawa da suka shude. A zahiri, yau tana jan hankalin miliyoyin mutane, ba kawai daga cikin Iraki ba amma a duk faɗin duniya.
A yau tattakin Arbaeen ya zama daya daga cikin alamomin Musulunci da kuma dalilin yada sakon Musulunci don haka ya kamata a girmama shi a matsayin daya daga cikin alamomin Ubangiji (SWT).
©Freeddom Fighters NG
1 Comments
Allah yasaka da Alkhari
ReplyDelete