A cikin Sahihu Muslim, akwai wata shahararriyar hadisin da Ibn Abbas ya ruwaito yana cewa: Kwanaki uku kafin wafatin Annabi Umar bn Khattab da sauran sahabbai suna wajensa. Sai Manzon Allah (saww) ya ce, “To, bari in rubuta muku wani abu, wanda ba za ku bace da shi a bayana ba. Sai Umar ya ce: “Annabi ya kamu da rashin lafiya, kuma muna da Alkur’ani Littafin Allah, ya ishe mu.
Maganar Umar ta haifar da cece-kuce a cikin wadanda suke nan. Wasu suna cewa a bi umurnin Annabi domin ya rubuta duk abin da yake so ya rubuta don shiriyarsu. Wasu kuma suka goyi bayan Umar. Yayin da tashin hankali da hayaniyar suka tsananta, sai Annabi ya ce: “Ku tafi ku barni!" Don haka Ibn Abbas ya kasance yana cewa: “Abu ne mai muni, matuqar muni, ace abin da ya faru na sabannin ra’ayi da hayaniyar jama’a ya shiga tsakanin rubuta wasiyyar Annabi, saboda haka Annabi bai samu damar rubuta abin da yake so ya rubuta ba a takarda."
Ya zo a cikin Rawdatul-ahbab cewa Annabi ya ce wa Fatimah: “Ki zo mini da ‘ya’yanki”. Fatima ta zo Hasan da Husain wajen Annabi. Su biyun suka gaisa da Annabi, suka zauna a gefensa suka yi ta kuka don ganin halin da Annabi yake ciki ta yadda mutanen da suka gan su suna kuka sun kasa lallashin su. Hasan ya dora fuskarsa a kan fuskar Annabi, Husaini ya dora kansa bisa kirjin Annabi.
Manzon Allah (saww) ya bude idanunsa ya sumbaci jikokinsa cikin so da kauna, yana umurtar mutane da su so su da girmama su. A wata ruwayar kuma, an bayyana cewa sahabbai da suke wurin, da suka ga Hasan da Husaini suna kuka, sai suka yi kuka mai karfi, har Annabi da kansa ya kasa rike hawayensa saboda bacin rai. Sai ya ce: Ku kira mini dan uwana Ali. Ali ya shigo ya zauna kusa da kan Annabi. Lokacin da Annabi ya daga kansa, Ali ya koma gefe, ya rike kan Annabi, ya kwantar da shi, a kan cinyarsa. Sai Annabi yace:
Ya Ali! Na karbo wani adadi daga wajen Bayahude wane da wane don ciyar da rundunar Usamah. Ka tabbatar ka biya. Kuma ya Ali! Za ka zama mutum na farko da zai isa gare ni a tafki na al-Kausar. Za a kuma ba ka wahala mai yawa bayan rasuwa ta. Ka yi hakuri kuma idan ka ga mutane sun fi son sha’awar duniya, ka fifita lahira”.
A cikin Tarikh-al-Khamis kuwa, an ambaci cewa Muhammad ikn Ishaq ya ce:
"Annabi ya rasu ranar litinin kuma an binne shi a daren Laraba."
Da yake kimanta shekarunsa, Abul-Fida’ ya rubuta:
"Ko da yake akwai sabanin ra'ayi game da shekarun Annabi, amma duk da haka an lissafta shi daga sanannun hadisai, ya bayyana ya rayu tsawon shekaru 63."
0 Comments