Daga Shamsuddeen Adamu Al-shirazy
05 ga Octoba, 2022
Bayan Shekaru 3 da kashewa tare da tsare Gawarwakin mabiya Shaikh Zakzaky, ƴan Sanda sun saki gawarwaki 3 cikin 9 na Ma su Jerin gwanon neman asaki Shaikh Zakzaky (jerin gwanon Free Zakzaky).
A cikin wata sanarwan manema labarai wanda mai magana a madadin Daddalin Ɗalibai na Harkar Musulunci ƙarƙashin jagoranci Shaikh Zakzaky ta fitar, Halima Aliyu ta bayyana cewa Ƴan Sandan sun kashe masu jerin gwanon neman asaki Zakzaky ne a ranar Litinin, 22 ga Yuli, 2019 a Sakatariyar Tarayya Abuja, a lokacin da suke gudanar da jerin gwanon nuna rashin amincewarsu da tsare mai shugabansu Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibraheem ba bisa ka’ida ba.
Jami’an ‘yan sandan sun kai farmakin ne tare da bude wuta kan masu jerin gwanon, lamarin da ya kai ga kashe masu jerin gwanon 12, wani mutum 1 da ba a san ko su waye ba, Usman Umar (Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda) da kuma Precious Owolabi (dan jarida na gidan talabijin na Channels TV).
Halima Aliyu ta cigaba da cewa, "A yayin da ake tsare da masu jerin gwanon neman asaki Shaikh Zakzaky a gidan yari, mutane 3 sun rasa rayukansu, kuma an kai gawarwakin zuwa Asibitin Asokoro. Jimillar mutanen da Ƴan Sandan suka kashe 18 ne da suka hada da masu jerin gwanon 15, ɗan Sanda 1, ɗan jarida 1 da kuma mutum 1 da ba a san ko su waye ba.
A ranar Talata 4 ga Oktoba, 2022 ƴan Sandan su saki gawarwakin masu neman asaki Shaikh Zakzaky waɗanda suka haɗa Shaheed Suleiman Shehu, Shaheed Bilyaminu Abubakar Faska, da Shaheed Yakubu Yahaya Faska.
Cikin kalamanta, Halima Aliyu ta bayyana cewa "Ya zuwa yanzu dai akwai gawarwakin masu jerin gwanon neman asaki Shaikh Zakzaky 6 a hannun ƴan Sanda kuma mun sha alwashin ci gaba da fafutukar ganin an sako dukkan gawarwakin.
0 Comments