Muna Shawartar Masu Zuba Hannun Jari a Kasar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (Dubai) Ku kwashe Hannayen Jarinku Domin kada kuyi Asara | Brigadier General Yehya Saree



- Mahadi Tukur Almizan.


Adaidai lokacinda wa'adin tsagaita wuta tsakanin Yemen da Saudiyya da kawancenta yazo karshe a ranar Lahadin data gabata, mai magana da yawun rundunonin sojan Yemen Birgediya Janar Yehya Saree ya baiwa 'yan kasuwa masu zuba hannun jari a kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) wato Dubai shawarar cewa su kwashe dukkanin hannayen jarinsu daga wadannan kasashe zuwa wasu kasashe masu aminci domin kada suyi asarar dukiyarsu.


Agefe guda kuma Majalisar dinkin Duniya na cigaba da kokarin ganin ankara kulla wata yarjejeniyar ta tsagaita wuta, dukda kokarinda sukayi tayi na ganin antsawaita wannan yarjejeniyar tsagaita wutar kafin karewar wa'adin, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres yabayyana rashin jindadinsu gameda kin tsawaita yarjejeniyar da bangarorin buyi sukayi.

Post a Comment

0 Comments