YADDA SHARI'AR SU MAL HARUNA ABBAS, IBRAHIM HUSSAIN DA ADAM SULAIMAN HUJJA TAGUDANA JIYA LARABA



Daga Ado Sahifa Zaria

Kamar yadda muka sani yau ne ranar da aka sanya domin ci gaba da sauraron shari'ar da akeyi tsakanin gwamnatin tarayyar Nigeria da yan uwa su uku. wadanda ake tsare dasu tun shekarar 2013 yau kimanin shekaru goma kenan ana tsare dasu bisa zalunci.

A yau laraba 26 ga watan  10 / 2022 ga kadan daga cikin abinda ya gudana a kotun. bayan an kira kes din sai lauyan DSS yace yau basu shirya ba don haka a daga. Sai lauyan su Mal Haruna Abbas, Barrister Ali Yawuri ya mike yace mu a shirye muke kuma har mun shigar da takardar neman beli.
Sai Alkali yace shi a yau bazai saurari maganar beli ba saboda akwai shari'o'in zabe a gabansa. daga nan kuma sai lauyan gwamnatin ya mike yace suma sun shirya a ci gaba da shari'ar. sannan kuma sai  yace yana neman kotu ta daga sauraron shari'ar nan domin yanada wani muhimmin aiki na gwamnatin tarayya da zaije a garin Lagos. 
    To anan sai Lauyan yan uwa Barrister Bello Ibrahim Jahun ya mike yace. yana jawo hankalin  alkali da yayi la'akari da halin da su Mal Haruna Abbas suke ciki na rashin lafiya tsawon shekaru goma suna tsare ba tare da an kawo wata shaida ko wata kwakwarar hujja ba. sannan kuma da shi lauyan gwamnati yace zai je National assignment , ai wannan shari'ar ma National assignment ne, domin suma yan kasa ne. kuma duba da yanayin tabarbarewar harkar tsaro a kasar nan komai na iya faruwa dasu ko yan uwansu da suke shigowa motoci su zo kotu. 
    To sai Alkali yace yana sane da halin da suke ciki amma zai yi kokari yayi wani abu kafin karshen wannan shekarar. 
      Sai Barrister Ali Yawuri ya mike yace, Alkali ya kamata fa kayi adalci. wadannan mutanen shekaru goma fa suna tsare ga halin rashin lafiya.  wannan batun zabe da kakeyi ai bayan shari'ar nan ne, akayi. 
   Sai Alkali yace gaskiya ba zan saurari maganar beli yanzu ba. sai na gama hukunci akan shari'oin zabe. ai nine nace na amince ku rubuto maganar neman beli , don haka zan saurare ku ne bayan kammala shari'oin zabe. Idan na saurari maganar  belin nan naku to za'a tuhumeni zan fuskanci query.  domin haka na daga shari'ar zuwa 6/10/2022 .

     Anan sai Mal Haruna Abbas da Ibrahim Hussain suka daga hannu alamar sunada magana kenan.  Sai Lauyan su yace mutanen  sa sunada magana .

     Sai Mal Haruna Abbas  Ali ya mike yace : ina kira gareka Alkali ka dubi halin da muke ciki na rashin lafiya.  sai  Alkali yace gidan yarin basa kulawa da kai ne ? Sai Mal Haruna Abbas yace basa kulawa dani nike kulawa da kaina a dawainiyar magunguna da sauransu.  Mal Haruna yace yau kimanin shekaru goma kenan ana tsare damu amma ba'a samemu da laifin komai ba. ance mu barazana ne gwamnatin America da Isra'ela da gwamnatin Nigeria. amma ka san yan Boko Haram sun kawo hari gidan yarin Kuje da muke ciki sun balle kofofin gidan kowa ya fita. babu jami'an tsaron yan  sanda da squard din sojoji da warders a gidan yarin da wajen gidan yarin na tsawon awoyi biyar.  amma bamu gudu ba, idan da mu barazana ne ga wata America da Isra'ela da gwamnatin Nigeria ai da mun gudu kuma baza a iya sake kama mu ba. amma sauran mutanen duk sun  gudu , mune muka ce wasu su tsaya kuma suka tsaya. sai jikin Alkali yayi sanyi. 
  sannan Mal Haruna yace mu fes muke bamu da laifin komai, kuma masu laifin ma da aka kawosu wannan kotun ai bada belin su kayi saboda basu gudu a gidan yarin ba. to mu me mukayi muku ne ? 

    Ibrahim Hussain ya mike yace: ya mai shari'a  wannan abinda Lauyan gwamnati ya fada cewa zashi National assignment duk shiri ne ma'ana ( game ) ne. sai lauyan gwamnati ya harzuqa yace ya zaice wasan kwaikwayo ne aikinsu. sai Alkali yace ma lauyan gwamnati kayi haquri kasan a fusace yake. sai lauyoyin su Mal Haruna Abbas suka cewa lauyan gwamnati ai ba da kai yakeyi ba.

Sai lauyan gwamnati yace ai mun tattauna da Barrister Ali Yawuri akan maganar beli. Sai Alkali yace ma lauyan gwamnati ka sanar da magabatanka domin ayi a gama.
     Sai Ibrahim Hussain yace dashi nakeyi ai ya san na san  shi domin ai sun nemi in zame musu shaida a kan wannan shekarar naqi. domin haka dukkan abinda suke shiryawa na san shi sarai. kuma ko kotunan baya irin wannan karyar sukeyi suce sunada National assignment sai ai ta daga shari'ar shi yasa muka kawo yau dinnan ba'a gama Shari'ar ba. amma an kawo masu laifi da yawa wannan kotun kuma an bayar da belin su. domin haka zan dena zuwa kotun nan idan aka ci gaba a haka. 

Sai Alkali Emeka Mwyhite yace : duk na lura da halin da kuke ciki , amma  ai baku dade a kotu na ba , kuma bana yawan daga muku shari'ar nan baifi sau biyu ba na daga.   shari'ar ba. idan aka dawo kotu zan saurari muhawara akan beli da batun shari'ar nan . ku kwantar da hankalin ku.

Post a Comment

0 Comments