Ta'addancin Sojojin Guard Brigade Akan Masu Tattakin Arba'een a Shekarar 2018.



 29 October Ranar Tinawa Da Waki’ar 29 October 2018

-Asperger 29/10/2022


A wurin mu rana ce ta juyayi rana ce da maƙiya Allah suka aiwatar da harin da tin bayan waki'ar Buhari ba'a sake ta'addanci kamar shi ba, a ranar sojojin Guard Brigade dake tsaron fadar shugaban kasa suka aiwatar da mummunan hari kan almajiran Shaikh Ibraheem Ya'qoub El-Zakzaky (H) masu Tattakin Arba’een na Imam Hussain (AS) a daidai gadar Karo (Karo Bridge) Abuja.


Sun kashe mutane 52 tare da jikkata adadin masu yawan da ba zasuyi kasa da 50 ba nan take, a ciki sun kwashi wasu da rai zuwa barikinsu acan suka kashe da dama cikinsu hanyar azabtar dasu, caccaka wuka, wuta, da sauran nau'i na azaba, basu tsaya nan ba washe gari 30 October sun sake bude wuta kan taron Arba'een na Imam Hussain (AS) da aka sake fitowa a cikin tsakiyar garin Abuja sun kuma kashe tare da raunata da dama a ranar.


A wannan rana ta 29 October tayi daidai da cikar shekaru 4 da wannan ta'addaci da gwamnatin mulkin kama karya ta Manjo Buhari Janaral Dolo da Bindiga ta aiwatar, muna addu'a Allah (T) ya kara daukaka daraja ta shahidan mu da suka bada jininsu ga Imam Hussain (AS) a wannan waki'ar, Allah ya ƙara la'anta da tsinuwa ga makasansu, Allah ya raba su da abinda suke nema a duniya gobe ƙiyama ya dawwamar dasu cikin azabar shi ya rabbala alameen.

Post a Comment

0 Comments