Akan Shahadar Sayyida Zahra Salamullahi Alaiha.

 



Tarihi ya bayyana Lokacinda Imam Ali yake yiwa Sayyida Zahra wanka ya ji hakarkarinta/Awazarta a karye duk jarumtan Imam Ali sai da ya zubarda kwallah yayi kuka da sauti mai ban tausayi da tayarda hankalin mai sauraro.


Sayyida Zahra ta dauki tsawon lokaci a wannan yanayin Awazunta a karye ba tareda ta sanarda kowa ba sai lokacinda Imam Ali yazo yimata wanka sannan har akasan cewa awazunta a karye suke.


Wah Museebata 

Ya Zahra.


Sannan Imam Ali (As) Yayinda Yazo Sanya Sayyida Zahra (SA) Aƙabari Yana Kuka Yace "Ya Rasulullah Kabarmin Ɗiyarka Lafiya, Amma Yau Ina Dawo Ma Da'ita Cikin Raunuka Da Tabo!"💔😭


Sayyida Zahra ta shafe kwanaki kusan 95 awazarta a karye ba tareda ta sanarwa da kowa ba dan'uwa ka auna kaji zafinda kakeji idan ka goce a hannu ko a kafa wanneh irin radadi kakeji?


Toh Sayyida Zahra watanni ta kwashe awazunta a karye ba tareda kowa ya sani ba.


Hakika an zalunci Sayyida Zahra Makurar zalunci.


La'antar Allah ta kara tabbata ga makasanki Ya Zahra.


Allah ya kara nunka azabarka ga makasan Ummul Hasanain.


©Freedom Fighters NG.

Post a Comment

1 Comments

  1. Rabbi Salli ala Muhammad wa'ali Muhammad adadin halittun ubangiji.Allah ya la'anci duk Wanda keda hannu akan zaluntarta da duk mai goyon bayan haka Amen ya Rabbil'alamin.

    ReplyDelete