ALLAH TA’ALA YA SANYA DUNIYA TA ZAMA GIDAN JARABAWA

 


Mai yiwuwa mutane za su kasa gane me yasa ya zama su zababbun Allah su kan sha wahala? Hikimar wannan shine, Allah Ta’ala dama ya shirya wannan gida na Duniya domin jarabawa ne, kuma daidai gwargwadon daraja daidai gwargadon musiba. Kamar yadda ya zo a Hadisi Manzon Rahma (S) yana cewa: “Manya manyan darajoji suna tare da manya manyan musibobi.” Ya kuma ce: “Tunda Annabawa su suka fi daraja, su suka fi kowa shan wahala. Tunda kuma shine shugabansu to shi ya fi kowane Annabi shan wahala.”


To, da akwai wata hanya da a kan bi a samu daraja ba tare da an sha wahala ba, to da ita wannan hanyar Manzon nan (S) ya bi. Da Allah Ya biyar da shi ta wannan hanyar ba tare da ya sha wahala ba, saboda gatancin da yake da shi a wajen Allah. Amma saboda shi Allah Ta’ala haka ya shirya, yana daukaka mutane ne ta hanyar gwada su da musibobi. 


To, shi yasa ya zama hanyar dai kenan. Shi yasa Manzon Rahma (S) ya sha wahala. Ya shekara 13 a Makkah yana kira ana cutar da shi da nau’o’in cuta daban-daban, ya yi hijira zuwa Madina aka bi shi da yakoki, aka bi shi da Badar da Uhud, da Handak, bayan nan kuma da ya zo shiga Makkah domin shiga Umra aka rutsa da shi, aka karata a yarjejeniyar Hudaibiyya. 


Kama-kama har izuwa bude Makkah, musiba bayan musiba ne. Bayan bude Makkah ne ma aka yi Hunain, wanda shima aka ga marhaloli daban-daban, har izuwa lokacin da Manzon nan ya bar duniya aikin kenan. Ita kuma Sayyida Zahra (SA), wafatinsa (S) ke da wuya kuma sai musibobin da ya samu Ahlulbaiti (AS), wanda mu kan fade su a lokutansu.


Rubutawa: Cibiyar Wallafa.


Photo: Freedom Fighters Ng.

Post a Comment

0 Comments