–Shaikh Ibraheem Zakzaky(H)
"Izzan mu na tattare da mu ne, mu tsaya ƙyam mu bayar da Rayukan mu da Dukiyoyin mu domin ganin Addinin Allah ya tabbata, sannan sai Allah ya kawo taimakonsa. Dole sai mun yi, kar ku ɗauka abin (Addini) zai bayyana ne da kansa, bafa zai bayyana ne da kansa ba. To kuma sunyi shekaru shiru suke ji har sun ɗauka sun mallaki duniya yanzu sai yadda suka so, To wannan yunƙurin da suka ga ya ɗago sai suka ga ashe al'amarin ba haka ba ne, matukar akwai yunƙurin nan yana nufin akwai wata Rana ƙarshensu zai zo kenan."
"Saboda haka ne ka ga kuma suna yin baji ba gani baza suyi da wasa ba. Dazun Farfesa yana yin magana akan kisa, dama siyasar kenan iya kanta kenan. Har yanzu basu da wani strategies, strategies din Iblis ne, E "Faƙatilu Auliya'a Shaiɗan Inna Khaidi Shaiɗani Kana Da'ifa", shi Shaiɗan baida wani tunani illa akashe kawai, akashe-akashe shikenan."
"To kuma idan har mutum zai ji tsoron a kashe shi, to ko bazai iya komai ba sai ya kashe mutuwa, inya fi ƙarfin mutuwa to shine nasara, meye fin ƙarfin mutuwa?, shine yace gani akashe ɗin, ba gani akashen da suke cewa ba, ka tsaya akan addini ƙyam ka ce gani sai dai ku kashe ni."
"To ma ko baka tsaya akan addini ba labudda zaka mutu, watan wata Rana sai aji ance ka mutu, ko dama mutum ya rayu yayi kaza shikenan sai kaji ance kuma wata Rana ya mutu."
"Saboda haka, bai kamata mutum ya zamo mutum ya tsorata shi da mutuwa ba. To mun gwada musu mu ƴaƴane domin Qudus na bana duk waɗanda aka jima ciwo bara duk sai da suka dawo harda masu dogara sanda, harda wanda aka jima ciwo shekaru bakwai (7) da suka wuce suma sun bi Muzahara din ba abin da aka fasa."
– Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) A Ranar 25th July, 2015.
Rubutawa: Shamsuddeen Adamu Al-shirazy
©FREEDOM FIGHTERS NG
0 Comments