Harin ta'addancin rashin Imani da rashin Hankali da Sojojin Nijeriya suka aiwatar bisa umarnin shugaban ƙasa Buhari (L.A), karkashin jagorancin shugaban Sojoji mai Ritiya Tukur Yusuf Burtai Aranar 12-12-2015. Har Abada bazamu taɓa mantawa da wannan mumman harin ta'addancin da akai ma Jagora Sayyid Zakzaky da ɗinbin manyan Almajiransa da 'ya'yan sa na cikin sa ba. Dukkan wanda ya samu Shahada a wannan lokacin, lokacin sane yayi. Domin daga cikin mutanan da waƙi'ar ya rutsa dasu, wasu sunyi kwanaki acikin kwata, da shiga mawuyan cin hali mara daɗi. Akwai Wanda aka soka Masa mashi a wuyan sa! Allah Ta'ala bai gaddara musu Shadaba a wannan lokacin ba, Lallai Shahada lokacin ne.
A wannan lokacin dukkan wanda suka gani sai sun kasheshi ko da ko jariri ne wanda besan ma meye duniya ba. Ga hujja Kamar haka: Lokacin da suke tsaka da ƙashe 'Yan'uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) a Zariya. Akwai wani yaro (Bayan an kashe mahaifiyar sa), ya taso yaga wani soja sai yaron yake furta cewa; "Baba-Baba" Haka wannan sojan babu tsoron Allah babu Imani ya sanya bindiga ya hargitsa ma yaron Harshashi masu rai. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Anyi zulunci mara misaltawa a garin Zariya, akan muminai raunana wanda basu riƙe da ko Allura.
Sojojin Nijeriya bayan sun kammala kashe ɗaruruwan mutane a Hussainiya Baƙiyatulla Zariya. Sannan Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufa'i Saida yazo cikin A.B.U yazo yaga irin aikin da sojojin suka aikata anan Hussainiya Baƙiyatulla. Sannan a lokacin Sai ya Kira Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), Yana tanbayan sa cewa yana gida? Jagora Sayyid (H), ya cema Eh! Sannan sojojin suka ƙarisa Gyallesu su shiga har cikin gidan Jagora Sayyid (H), bayan sun kashe kowa da kowa. Sannan su samu daman kaiwa ga Jagora Sayyid (H), dashi da iyalin sa.
Nan take su kashe 'ya'yan sa 2 domin cika umurnin da aka basu na na karshe Al-Zakzaky da Almajiran. Sannan nrn abu ne kamar yadda Sayyid (H) yake cewa; "Babu wata gwamnati da zata zo ba tare da anyi yarjejeniya tasa hannu akan kashe Al-Zakzaky ba." Da wannan nake kira ga 'Yan'uwa ku yaɗa saƙon ta'addancin da wannan Azzaluman Gwamnati tayiwa Jagora Sayyid (H) lungu da saƙo ta ko wace hanya da zaku iya, Ku kasance dani a rubutu na gaba.
©Ibraheem Y. Ibraheem
4-12-2022 (10 Jimadal Ula, 1444).
0 Comments