TUNAWA DA SHAHIDAN MU

 



Shekaru bakwai kenan tun watan Disambar shekarar 2015 da sojojin Nijeriya suka kai hari a Husainiyar Baqiyyatullah, gidan Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a Gyallesu, da Darul Rahma. Sun kashe mutane sama da dubu daya da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da mata 97 da 23 daga cikinsu na da juna biyu, maza 548, yara 193, da iyalai 39 gaba dayansu. Sojojin sun aikata munanan laifuka da suka hada da kona gine-gine, kona mutane da ransu, harbin jarirai, tare da biznesu a waje guda. 


Muhammad Rabiu Shuaib na daga cikin wadanda suka yi shahada. Hajiya Ummu Kulthum da Malam Abdussalam suka haisfe shi a ranar 6 ga watan Nuwamba 1986 a jihar Kaduna.


Ya halarci makarantar Alheri Nursery da Primary. Ya kammala karatunsa na Sakandare a Makarantar Sardauna Memorial College Kaduna, sannan ya ci gaba da karatun a Kaduna Polytechnics inda yake shirin kammala HND ajin karshe ya yi shahada a ranar 13 ga Disambar 2015. 


Ya kasance mai himma wajen gudanar da ayyukan wannan harka, musamman ma  aiki da Dandalin dalibai. 


Allah ya karbi Shahadarsa.


@Szakzakyoffice 

#ZariaMassacre 

#OurMartyrsOurHeroes

07/12/2022

Post a Comment

0 Comments