- Sheikh Zakzaky (H)
"Har ma akwai ayar da take cewa ""Latajidanna Ashaddannasi adawatan, lillazeena amanu alyahuda wallazeena ashraku. Walatajidanna Aqrabahum mawaddatan lillazeena amanullazeena Qalu inna nasara , zalika bi'anna minhum qiseeseena, waruhbanan, wa'annahum la yastakbirun (Alma'ida, V-82)" Yace 'Zaka ga wanda suka fi kusa da son Muminai (wato Musulmi) in nace Musulmi za a fi ganewa, wanda suka fi kusa da son sune wanda suka ce mu Kirista ne'. Allah (S) yace saboda a cikinsu akwai Malamai, akwai masu ilimi kuma su basu da girman kai. Wannan yabo ne ga al'ummar kiristoci wato cikinsu akwai masu ilimi kuma basu da girman kai shi yasa su suka fi kusa da Musulmi".
"To nasan akwai wasu abubuwa da wannan ba shine muhallin su ba tunda wani lokacin muna taron Kirista da Musulmi ma yi wannan. Amma nasan akwai waɗansu ayoyin da wayansu suke musu fassara wani iri, alal misali akwai 'La tattakizul Yahudu wal Nasara auliya' na taba ganin wani fassara da wani ya rubuta da Ingilishi yace 'They not to take Jewish and Christian as Friends' sai yace to ai addinin ku yace kar ku dau kowa a matsayin aboki. To sam ba abin da ayar ke, shi kuskure ne ma a fassara shi da Friend (ba friend yake nufi ba)".
A lokacin su akwai yaƙe-yaƙe, akwai ƙasashe (akwai ƙasan Haibar da Fadak su Jews ne, akwai Najran da waɗansu ƙasashe su kuma Christian ne, akwai kuma su Musulmi a Madina, akwai kuma Quraishawa masu bautan gumaka), to lokacin da ake wannan yaƙe-yaƙe su Quraishawa sai suka hadu da Kiristoci da Yahudu suka haɗa kai against Annabi. To sai aka ce wannan ayar ba Friend ne ma'anan ta ba tana magana ne a wannan wad'in ne (tana cewa kar ku ɗauke su Ally) ma'ana kar ku ɗauki mutanen Fadak da Haibar da kuma Najran a matsayin a matsayin alies din ku, domin su they are Allie's to one another (not friends). Ga Fasto Yohanna Buru abokina ne koda yake shi yace wai Ni me gidansa ne, to amma ko kaɗan wannan wrong fassara ne, kawai situation ne na wannan lokacin tsakanin ƙasa da ƙasa".
– Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a shekarar 2014 a Hussainiyyar Baƙiyatullah Zaria. Ibrahim Almustapha Saminaka ya rubuto muku daga Bidiyon jawabin.
0 Comments