ZAMU DINGA TUNAWA DA SHAHIDAN MU BA IYA LOKACIN WAKI'AR BA

 


 — Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)


"Kullum za mu tuna da wadannan Shahidai, kuma za mu tuna da su ba a lokacin waki’ar kawai ba, a kowane lokaci, da yin addu’a gare su, da kuma zubar da hawaye. Wannan duk lokacin da na tuna da Shuhada din nan na kan yi hawaye. Har ma nace na kan dauki wani lokaci na yi wa kowane mutum daya kukansa na musamman. Na kan ambaci suna, iyakan wanda za su ambatu, sannan kuma na jimlata gungun mutane daban-daban wadanda waki’ar ta rutsa da su, sawa’un a kan hanyarsu na shiga gari ne, ko kuma a wasu wurare daban-daban da aka yi waki’ar."


 "To, muna fatan kuma Allah Ta’ala ya karbi wadannan wadanda aka kashe a matsayin Shahidai. Ya riskar da su da rayayyu wadanda ake azurtawa. “”Ahya’ul marzukin” kenan. Ya zama suna raye a wajen Allah ana azurta su. Kuma muna rokon Allah ya dawo da su a lokacin bayyanar Alqa’im (AJ). Muna rokon Allah ya dawo da su su zama sun ba da gudummawarsu wajen yin yaqi gaba gare shi."


 – Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a cikin jawabinsa na tunawa da shekaru 6 da Waki'ar Buhari a shekarar 2021.

Post a Comment

0 Comments