1. Yana daga cikin Mujarrabatu na As-Sheikhul Mufid (R.A) dangane da Neman Arziki, a cikin Watan Rajab Mai alfarma, karanta wannan Ayar sau 7:
(الله لطيف بعباده
يرزق من يشاء وهو القوي العزيز)
.
Sannan a karanta wannan Addu'ar ita ma sau 7:-
اللهم أدم نعمتك والطف بنا فيما قدرت علينا
"Allahumma adim ni'imataka walduf binaa fiimaa qaddarta alaina"
.
2. Haka ma Al-Allamatu As-Sheikh Muhammad Taqiy Al-Isfahaaniy (R.A) ya naqalto a cikin Littafin Miftaahussa'adati daga sashin Manyan Malamai cewa:
Duk wanda ya karanta wannan Ayar sau 12 kullum a cikin Watan Rajab
(الله لطيف بعباده
يرزق من يشاء وهو القوي العزيز)
Babu Shakku zai zama mai wadatar dukiya, ya ce hakika Mazaje abin la'akari kamar Muhammad Bakir Addamaad sun jarraba hakan. Kuma ya kara da cewa a wannan zamanin namu ma jama'a da dama sun jarraba hakan kuma duk sun samu wadatar dukiya.
.
ISHAQ MUHAMMAD ISHAQ.
.
1 Comments
Allah ya biya. Ama taimaka ayi mana transliteration na wannan aya. Ko kuma a rubuta mana sura da lamba aya din.
ReplyDeleteDomin ba kowa zai iya karanta Rubutun da babu wasali ba.
Muna godiya.