Sayyid Abul-Fadhal Abbas [AS] an haife shi a Madina, ranar 4 ga watan sha’aban, shekara ta 26 bayan hijira, Sayyid Abbas a cikin ‘ya’yan Imam Ali [as] maza baya ga Imam Hassan da Imam Husain[AS] ba wanda ya kai shi daraja.
Sayyid Abul-Fadhal Abbas[as] tanadi na musammam wanda Imam Ali[as] yayi ma Imam Husain [AS] domin waki’ar karbala, domin yazo a tarihi cewa lokacin da Imam Ali [as] yayi nufin yin auren ya bukaci dan’uwansa Akil dan Abi dalib, [da yake shi masanin nasabar larabawa ne] daya sama masa mata wadda ta fito daga gidan jarumai, domin ya aure ta,da fatan ta Haifa masa a jarumi, wanda zai taimaka ma Imam Husain [as] a karbala, sai Akil yace masa ga Fatima ‘yar Hizam.
Yazo a tarihi cewa gidan su gidan jaruntaka ne, Imam Ali [AS] ya amshi wannan Magana tasa, saboda haka sai ya sa shi a madadin sa, domin neman auren ta a wajen mahaifin ta. Akil ya tafi wajen baban ta, ya gabatar da wannan magana gareshi, jin haka nan take mahaifin ta ya amsa maganar kuma yayi farin ciki mai yawa.
Yazo atarihi cewa lokacin da Akil da mahaifinta suke wannan Magana, ita Fatima ‘yar Hizam tana labarta ma mahaifiyar ta wani mafarki da tayi cewa tana zaune a gida sai taga wata ya fado a gidan su, bayan haka kuma sai taurari hudu suka biyo bayan sa.Ta gama fada ma mahaifiyar ta kenan wannan mafarki, sai ga baban ta ya shigo cikin gada da wannan albishir, na cewa Akil yazo da maganar neman auren Fadima ga Imam Ali [AS] jin haka sai mahaifiyar tace masa ai ga mafarkin da ta bani labari dashi yanzu, lokacin da baban ta yaji bayanin mafarkin da tayi, ya dada farin ciki, har yake cema ‘yar tasa “Lallai Allah ya tabbatar da wannan mafarki naki, ina taya ki murnar samun sa’adar duniya da lahira” Bayan da akayi auren,ta tare gidan ImamAli[AS] lokacin da akayi auren yazo a tarihi cewa tana da kusan shekaru 20 ne,kuma yazo a tarihin ta cewa a daren farko data shiga gidan Imam Ali[AS] tace masa tana da wata bukata, ImamAli[as] yace miye bukatarki? Tace masa ina so in zaka kira sunana, kada ka kirani da sunana Fadima,saboda jin sunan zai dunga sa,su Hassan da Husain da Zainab, su dunga tuna mahaifiyar su, wanda hakan zai dunga sosa masu rai.
To sai Imam Ali[AS] tun daga lokacin,yakan ce mata ummul-banin,saboda haka wannan kinaya shi yasa mata shi, wato tun kafin ta haifi ‘ya’yan ta maza guda 4. sune Abbas,Abdullahi, Ja’afar da kuma Usman. Imam Ali [as] yace nasa masa suna usman, saboda tunawa da sunan usman dan maz’un,Usman dan Maz’un sahabi na Manzon Allah [S] ne, kuma ya rasu tun manzon Allah [S] yana raye, saboda haka sunan ba yana komawa bane ga sunan usman dan Affan bane kamar yadda wasu zasu yi tsammanin haka.
Mahaifiyar Sayyid Abul fadhal Abbas ta kasance mai kulawa da kuma girmamawa ga Imam Hassan da Imam Husain[AS] akwai ma lokacin da take cema ‘ya’yan ta kada ta kuskura taji wanin su yana kiran Hassan ko Husain da sunan sa, sai dai suce ya shugaba na.
kuma yazo a tarihin ta cewa ta kasance yadda take nuna so da kulawa da kuma kauna ga ‘ya’yan sayyida Fadima [AS] ko ‘ya’yan ta bata yima haka, kuma zamu ga haka a aika ce a rayuwar ta, bayan shahadar su Imam Husain[AS] lokacin da labari yazo madina na cewa an kashe su, wanda yazo da labarin da yake yi mata ta’aziyyar ‘ya’yan ta, daya bayan daya, abinda take tambayar sa miya samu Husain? yana fadin an kashe Husain, sai ta fashe da kuka. Akwai ma wani malami da yake cewa a tarihi ba a samu wata kishiya ba, da take fifita ‘ya’yan kishiyar ta akan ‘ya’yanta kamar ummul banin, wannan dai ya nuna irin gayar biyayya da kuma wula’a da ummul banin take dashi ga Ahlul-bait[AS]Kuma yazo cewa lokacin dasu Sayyida Zainab[as] suka dawo madina, ta kaima ummul banin ziyara ta musammam domin yi mata ta’aziyyar shahadar ‘ya’yanta, wato sayyid Abbas da kuma kannan sa ukku, Ga shekarun ko wannan su lokacin da yayi shahada, Sayyid Abul fadhal Abbas 34,Abdullahi 25, Usman 21,Ja’afar 19.
Kinayar sa: Anai masa kinaya da Abul-Fadhal, saboda yana da da wanda ake cema Fadhal har wala yau anai mai kinaya da Abul-kasim, shima saboda dansa mai suna Kasim, yazo a kan cewa shima Kasim din yayi shahada a karbala. mu duba mu gani wannan waki’a ta karbala, kusan ko wane gida ta shafi iyaye da ‘ya’yayen su.Lakubban sa; Sayyid Abbas yana da lakubba masu yawa, amma wadanda suka fi shahara sune, Kamaru bani Hashim, wannan kuma saboda gayar kyawan halitta da Allah[T] yayi masa. Babul-hawa-ij, wato saboda yadda mutane suke samun biyan bukata idan suka yi tawassili da shi ga matsalolin su, kuma tabbas haka ne duk wanda yake da wata bukata, yayi tawassili da shi da iklasi, to Allah[T] zai biya masa bukata. Hamilu-liwa’a,a nai masa lakabi da wannan, wato madaukin tuta, da yake a waki’ar karbala a ranar Ashura shine Imam Husain [as] yaba tuta, kuma tuta ko rike ta musamman a lokacin yaki wani abune wanda yake da asali da kuma tarihi a wannan addini na musulunci, Alal misali a duk yakokin da Manzon Allah [S] yayi akwai marikin tuta a yakin, misali a yakin farko da Manzon Allah[S] yayi wato yakin Badar marikin tutar shine Sayyiduna Hamza, a sauran yakokin da Manzon Allah [S]yayi marikin tutar shine Imam Ali [AS] saboda haka Abul fadhal a ranar Ashura,shi yake dauke da tuta. kuma sai da takai yana rike da tutar da hannun dama, aka sare hannun,ya rike ta da hannun hagu, aka sare hannun hagun,ya rike da kirjin sa, kuma lokacin da wannan abu ya faru ba kowa daga shi sai Imam Husain[AS] da yake duk sauran mazajen an kashe su. Kuma tutar da take kubba din haramin Imam Husain[AS] tana alamta tutar da Imam Husain[as] ya ba sayyid Abul-fadhal Abbas[as] ne,kuma a kan canza ta duk shekara ne,a watan muharram, idan aka canza a kan yi kyauta da wadda aka cire ne.To Alhamdulillah wadda aka cire bana an baiwa Malamin mu kuma Jagoran mu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini,Sayyid Ibrahim Zakzaky[H] Kuma wannan tuta da take haramin Imam Husain[AS] itace wadda Imam Mahdi [AS]Zai yi amfani da ita,idan ya bayyana,domin daukar fansa akan waki’ar karbala da kuma tabbatar da addini a bayan kasa baki daya.
0 Comments