“Duk Mutane Sun Zaƙu Azo Ayi Zaɓe Su Samu Sauyi”

 



—Inji Sheikh Ibraheem Zakzaky [H].

“Har wala yau sun kasa gane juyi da akeyi (Juyin juya hali) ba juyin mulki bane‚ sauya tunanin mutane ne. Su mutane ne suke canjawa to‚ in sun canja dole gwamnati zata zama irin sune. Amma in an canja gwamnati Nizamin yana nan duk abu ɗaya ne.

Yanzu duk canje-canjen gwamnatin nan da ake tayi kunga ban-ban ci ne? Nizamin yana nan daram kuma sai daɗa lalacewa yake tayi, kuma duk mutane sun zaƙu cewa ainihin azo ayi zaɓe su samu sauyi tunanin da sukayi ada can ko? Sai kuma abin da suka zaɓa ya zama musu abin daya zama musu, to‚ kuma mai yuwuwa in sunyi zaɓen a sake ganin abin da ake gani yanzu.

Amma abin da ake ce muku shi Nizamin yana nan to‚ mu Nizamin da yake iko ba gyara shi za kayi ba‚ don bazai gyaru ba, yana buƙatar gaba ɗaya a ajeshi waje guda ne, a ɗauko sabon Nizami a koma akai.”

“Kuna tunanin kullum a kawo wai shugaba ne wanda zai yi. Zan baku wani misali: Kunga giya sannaniya ce cewa ta haramta ma musulmi‚ kuma akwai hadisin daya nuna cewa Allah ya la’anci kaman mutum bakwai dangane da giya. Damai dafawa, damai rabawa, da mai sayarwa, damai sha, damai dakon ta dama abin da akayi dakon shima kanshi abin da aka ɗauki giyar shima an la’ance shi.

Misali: Sai ga wani gidan dafa giya. Inda ake kasuwancin giya, sai akace Alhaji wane ne manaja, se ace yadda za’ayi mu samu Alhaji wane in yazama manaja ɗin zai san yadda zai yi ya rage giyar to, indai mutum ya zama manajan gidan dafa giya sunan sa mene? Sunan sa me dafa mene? To, kaga ya shiga cikin gungun da'aka la’anta to‚ amma muna tunanin in shine ya ɗan hau zai ɗan gyara zai ɗan rage ‘Production’ gashi abu ya saɓa ma ƙa’ida amma sai kana tunanin atafau musulmi mutumin kirki yahau ya gyara shi bazai yuwu ba.”

—Jagorana Sheikh Ibraheem Zakzaky [H] cikin jawabin Ziyarar Ɗaliban Hauzar Iraq, Ranar 10/05/2022 A Gidan Sa Dake Abuja.

  ©..Thr/18/02/2023
©...Ibrahim Y. Ibrahim ✍️

Post a Comment

0 Comments