Ranar Haihuwansa:13 ga Rajab 16H, acikin Ka'aba (Makka)
Ranar Wafatinsa:21 ga Ramadan 40H.
Gurin Ƙabarinsa: Masallacin Imam Ali (Najaf, Iraq).
Matansa:
Fatimah bnt Muhammad
Umaimah
Zainab
Ummul-Banin
Khawlah bint Ja'afar.
Ƴaƴansa:
Sunkai 35 ko 38 saɓanin ruwayoyi.
Mahaifansa:
Abu Talib ibn 'Abd al-Muttalib
Fatima bint Asad
Alkunyarsa: Abu al-Hasan
Imamancinsa: Shekara 29 (11-40 H).
Tarihi yazo cewa, an haifi Imam Ali ne acikin dakin Ka’aba a Makka, kuma ɗan kabilar Kuraishu ne. Mahaifin Imam Ali kuma kawun Annabi Muhammad (SAW), Abu Talib ibn ‘Abd al-Muttalib, shi mai kula da Ka’aba ne, kuma shehin Banu Hashim ne, wani reshe ne mai muhimmanci na kabilar kuraishawa.
Mahaifiyarsa Fatimah bint Asad ita ma daga Banu Hashim ce. A Al'adar Larabawa babban abin alfahari ne ga Imam Ali kasancewar iyayensa biyu duka Banu Hashim ne.
Haka nan Imam Ali yana ɗaya daga cikin zuriyar Isma’il ɗan Ibrahim.
A lokacin ƙuruciyarsa, Imam Ali yayi shekaru shida na farko a ƙarƙashin mahaifinsa. Sa'an nan,Annabi Muhammad(SAW) ya tambayi kawunsa, Abu Talib, yace yabashi Imam Ali, yazo ya zauna a gidansa. Hakan akayi. Lokacin da umurnin Allah yazo cewa Annabi Muhammad (SAW) ya fara wa'azi, wato ya sanar da Annabta, Imam Ali yana ɗan shekara goma kacal, shine namiji na farko daya bayyana goyon bayansa ga ɗan uwansa a fili, acikin kaf musulmin Makkah.
©FREEDOM FIGHTERS NG
Follow us @
🌎www.freedomdomfightersng.com
🖥️ t.me/freedom_fighters_ng
📲 https://twitter.com/F_FightersNG?t=CmT3abW2djBGGGuKOi1h2w&s=09
📸 www.instagram.com/freedom_fighters.ng/
📱www.facebook.com/109221621639457/
📞https://chat.whatsapp.com/D9T4vMofIQqGXGmDjTHJXp
0 Comments