بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل محمد.
Yau Alhamis 3 ga watan sha'aban ranace mai daraja, ranar da aka haifi limami na uku 3 wato Imam Hussain (as)
Imam Hussaini (as) shine ɗan Aliyu bn Abuɗalib bn Faɗimatuzzahra'u ɗiyar Annabin Allah (S), kani a wurin Imam hasanul-Mujtaba (s.a) sannan yaya agurin Zainabul kubrah (Ummul-masa'ib).
Shine khalifa na 3 a Imamai goma 12, wanda akema laƙabi da shugaban shahidai.
Alkunyarsa kuma Abu Abdullahi, an haifeshi ranar 3 gawatan sha'aban a cikin madina mai haske, yayi tsawon shekaru 11 yana Imamanci, yayi tsawon shekaru 57, yanada ƴaƴa maza 5 mata 3.
Da aka haifi Imam sai Manzon Allah ya daukeshi yana kuka sai Jibrilu ma yayi kuka tare da Sayyida Zahra (s.a) da Imam Ali (a.s) suka tambayi Manzon Allah (S) dalilin kukansa sai yace wannan shine wanda za'a kashe acikin takura a filin karbalah sai yakara da cewa:
إن ابنى، هذا إمام إبنى إمام أخى إمام أبو أئمة تسعة.
Wato wannann dan nawa Imami ne baban Imami dan uwan Imami kuma shine baban Imamai 9 dazasu zo abayanshi.
Yazo a ruwaya cewa "Manzon Allah (saww) yace "Husaini minni wa ana min Husaini" wannan daya ne daga cikin irin falalolin Aba Abdullah.
Yazo a ruwayoyi cewa Manzon Allah (SAW) yace "Imam Hassan da Imam Husaini su ne mafifitan mutanen duniya bayana da bayan mahaifinsu, kuma mahaifiyarsu ita ce mafi Alherin matan mutanen duniya, kuma Imam Hassan da Imam Hussain shugabannin samarin Gidan Aljanna ne.
قال الإمام الصادق (ع) :- احيوا امرنا رحم الله من احيى أمرنا….
وصلى الله على محمد وآل محمد.
Allah yasanya mu daga cikin masoyan Imam(a.s) kuma Allah yabamu shahada akan tafarkinshi madaukakiya.
Ali Ibrahim Ali & Zarah Kamal | Freedom Fighters NG.
©FREEDOM FIGHTERS NG
0 Comments