Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
An samu daga Imam Bakir da Imam Ja’afar da Ai’mma (AS) daban-daban cewa; idan ruwaya ta zo maka dangane da wani aikin alheri, in ka aikata, kana da ladan wannan abin da ka ji an gaya maka din, ko da ba haka Annabi ya fada ba. Saboda ita falalar Allah tana da yawan gaske.
Wato a babin falala ana amfani da hadisi, ko da bai inganta ba, ko da mai rauni ne. Hadisin da ba za a yi amfani da shi ba a babin falala kawai shi ne, ya tabbata kirkirarre ne. Hadisi Maudu’i, za a iya amfani da shi? Sam! Amma hadisi mai rauni, ba wani damuwa. In dai ya ce; wanda ya karanta kaza, za a ba shi kaza. Khalas! Karanta kawai, insha Allahu ka ma samu ka gama.
Saboda Allah (T) abin da yake da shi yana da yawan gaske. Bisa yalwar Rahamarsa zai ba ka wannan din. Yawwa! In dai aka samu ruwayar. Ballantana mu muna da ruwayoyi ma, wadanda suke ba a babin ‘ka’idu man balagah’ ba. Ainihin ma sun inganta ne ruwayoyin.
To, hatta ko ba su inganta ba a babin falala. Don wasu ka ga ni ban san abin da ya same su ba, da zaran watan wannan Azumin ya kama, su kuma sun fara wa’azi ke nan, kar a yi azumi. Wai azumin ana ce masa na tsofaffi. Wannan azumi ne na tsoho? Sun fara wannan abin ke nan. Ye-ye-ye, su yi ta ihu. Wai a daina yi. Wai Annabi bai yi ba.
Kuma sai su zo su ce; to, Annabi bai yi Rajab ba dai, amma ya yi Sha’aban. To, su kuma ba za su yi Rajab din ba, ba za su yi Sha’aban din ba. Amma sun dunga ke nan, suna cewa wadansu mutane sun kirkira ma kansu, suna yin azumin wata uku. Duk wanda ya yi haka nan, ya sabi Allah. Annabi bai taba wata uku yana azumi ba.
To, ‘falyakun’. Wa ya ce maka azumin ba kyau ne? Da Annabin bai yi ba, sai ya ce maka kada ka yi? Uhm? Da kake shan fura da nono, Annabi ne ya sha Fura da nono din? Da kake cin tuwo miyar kuka din nan, shi ma Annabi ne ya ci? To, ya ce maka kada ka ci ne? Ehen! Cewa Annabi bai yi ba, ba shi ne magana ba. Annabi ya ce; kada a yi?
To, ballantana an samu ruwaya. Su suna da ruwayar cewa; Annabi ya kasance ya kan yi azumin Sha’aban duk cikarsa, ya sada shi da Ramadan. Amma ba dayansu da zai yi. Yana nan yana sukan kar a yi Rajab. Amma Annabi yana Sha’aban. To, tunda yana sukar kar a yi Rajab, sai ya bar Rajab din, sai ya yi mene? Sai ya yi Sha’aban din. Amma ba zai yi wannan ba, ba zai yi wancan ba. To, wannan buzines dinsu ne. Su suka dauka ma kansu.
— Shaikh Zakzaky (H) ya yi wannan maganar a karshen wata watan Jimadal Thani, a shekarun baya a Husainiyya Baqiyyatullah.
0 Comments