MUNJI RADADIN ABINDA YASAMEKU, KUMA ZAMU CIGABA DA TAIMAKAMAKU | Sayyid Khamna'i ga Al'ummar Turkiyya da Syria.

 


A lokacin taron tunawa da mubayi'ar kwamandojin sojin saman kasar Iran ga Imam Khumain, Sayyid Khamna'i ya jajantama al'ummar kasar Turkiyya da Syria a bisa ibtila'in girgizar kasar data auku a kasashen biyu.


Sayyid Khamna'i yace " Jamhuriyar Musulunci ta Iran tayi bakin ciki a bisa faruwar wannan girgizar kasa wadda takai 7.8 na ma'aunin girgizar kasa (earthquake magnitude) a ranar Litinin".


Samada mutum 900 sun mutu a tsakanin kasashen biyu na Syria da Turkiyya.


"Hakika muna jajanta maku 'yan uwa na wannan kasashe biyu Syria da Turkiyya, munayimaku addu'a Allah (T) yayi rahama ga ruhikan wadanda suka rasu, kuma Allah yabaiwa iyalansu hakuri".


Yaciga da cewa " Muma anan Iran girgizar kasa tasha faruwa dan haka munsan yadda al'amarin yake, duk sanda girgizar kasa ta faru ana rasa masoya, lallai abune mara dadi dakuma daci a zuciya".


" Hukumomin Kasar Iran sun kai dauki kuma zasu cigabada kai taimako ga wadannan makotan kasashe biyu Syria da Turkiyya".


Wadannan sune kalaman Imam Khamna'i.


©Freedom Fighters Ng.


Rahoto: Wakilinmu, Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment

0 Comments