TUNAWA DA MUBAYI'AR KWAMANDOJIN SOJAN SAMAN IRAN NA SHAH GA IMAM KHUMAIN.

 


A rana mai kamar tayau 8 gawatan February na shekarar 1979 kwamandojin sojin sama na Iran na gwamnatin Shah sukayi mubayi'a ga Ayatullahi Khumain bayan yadawo daga gudun hijira daga Faransa.




A kowace ranar 8 ga watan February na kowace shekara ana gabatarda taron tunawa da wannan mubayi'a wadda ake kira (Homafaran Allegiance), a lokacin tunawa da wannan mubayi'a Jagora Sayyid Khmana'e yakan gana da jami'an sojin saman kasar na yanzu, a bana ma Jagoran yaganada wadannan jami'ai na sojin sama a birnin Tehran ayau Laraba.





Daga cikin maganganun dayayi a wajen taron tunawa da wannan mubayi'a, Sayyid Qa'eed yayi magana akan muhimmancin hadin kai ga al'ummar kasar ta Iran, yace " hadin kai yataka muhimmiyar rawa a lokacin juyin juya halin Musulunci da Imam Khumain ya jagoranta, Sayyid Qa'eed ya cigabada cewa " a yau ma munada bukatar karfafa wannan hadin kai  iyan iyawarmu".


A gefe guda kuma yayi gargadi ga Amerika da 'yan korenta akan makarkashiyar da suke shiryawa na ganin bayan wannan jamhuriyar Musulunci ta Iran.


©Freedom Fighters Ng.













Rahoto wakilinmu: Mahadi Tukur Almizan


📸Labari Cikin Hotuna

Post a Comment

0 Comments