ZA'A SAKI WASU DAGA CIKIN WADANDA AKA KAMA A ZANGA-ZANGAR IRAN | A bisa afuwar Sayyid Khamna'i.

 


A yau Laraba, anfara sakin wasu daga cikin masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Musulunci ta Iran, anfara wannan saki ne a bisa afuwar da Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Ali Khamna'i yayi.


Jami'an sashen kula da shari'a na kasar ta Iran daga yankuna daban daban na kasar sunje gidajen yari domin sanya ido akan yadda wannan sakin yake gudana ayau, wannan labari yafito ne daga kafar yada labaran sashen shari'a na kasar wato MIZAN NEWS.


Zuwa yanzu dai ansaki da dama daga cikin kamammun kuma za'a cigabada sakin wasu a cikin kwanakinnan .


Wannan afuwa dai bata shafi wadanda aka daure ba a bisa laifin kasancewa 'yan leken asirin kasashen waje ba, da sauran wadanda ake tuhuma da wadansu tuhumomi da suka shafi tsaron kasa.


Sanarwar wannan afuwa ta Imam Khamna'i dai ta fito ne a ranar da akayi bikin cikar Jamhuriyar Musulunci shekaru 44 da kafuwa, wadda tayi daidai ranar haihuwar Imam Ali Amirul-muminin.


Shugaban Kasar  Iran Sayyid Ibrahim Ra'isi ya yabawa Jagora Sayyid Khamna'i a bisa wannan dattako da yayi na afuwa .


©Freedom Fighters Ng.

Rahoto: wakilinmu, Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment

0 Comments