A SAN ABIN DA YA DACE:

 



- Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).


Ya kamata mu sani cewa wannan ba shi ne zai kai mu ga gyara ba. Kuma ko da za a ce misali mutane duk su ce wai Babangida 

ya sauka, in ya sauka wani wanda ya fi shi zalunci ne zai hau. 


Tunda haka al'amarin ya kasance. Lokacin Shagari, mutane suna 

ta cewa Shagari ya sauka. Yana sauka Buhari ya zo. Kuka ce kayya-kayya ai gara Shagari. To bayan an kau da Buhari, to yanzu kuma ana cewa gara Buhari. To idan ma yanzu Babangida ya kau, sai an ce ina Babangida?


Kamar mota ce ta rigaya ta lalace, sai ka ce ai direban ne bai iya ba, ka cire wannan ka sanya wancan. To in ba ka gyara motar ba ne babu 

yadda za a yi ta koma daidai, saboda ainihin lamarin ba direban bane, motar ce.


Don mu gane, dole sai tsari na adalci ne, zai iya tsayar mana da shugabanni masu adalci. Saboda haka ya zama kokarinmu shi ne mu tabbatar da tsari mai adalci. Dole kuma da 

ma tsari mai adalci sai shugabanni masu adalci (babu kuma wani adalci idan ba a cikin Musulunci ba!).


Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.


TAMBIHI: 


Ya kai mai karatu, kamar yadda muka ambata a gabatarwar wannan rubutun, cewa Shaikh Zakzaky ya yi wannan jawabin ne tun a shekarar 1992, a lokacin mulkin Babangida, don haka a qarshen maganarsa za ka ji yana ba da misali da koken ‘yan Nijeriya akan gwamma Shagari da Buhari (a mulkin soja), da aka hambare Buhari a wancan lokacin kuma mutane suka koma suna gwamma Buhari da Babangida! Kamar yadda Shaikh 

Zakzaky (H) a wancan lokacin yake cewa: “To idan ma yanzu Babangida ya kau, sai an ce ina Babangida?” Sak! Abin da yake faruwa kenan a yanzu, a yayin da kowannenmu shaida ne akan cewa, kullum aka zabi wata gwamnati sai an ce gwamma wacce ta gabace ta akan wacce take kai!


Mafitarmu daya ce, kamar yadda wannan bawan Allah ya kwashe shekaru kusan 40 yana shaida mana, cewa mun butulcewa Allah Ta’ala ne, mun qi bin tsarin da ya saukar mana, wanda a cikinsa ne yalwa da samun rahama madauwami suke, sai muka zabi mu bi wani tsarin da ba na Allah ba, muka ce Kwansitushin za mu bi, alhali ya haramta ma Musulmi ya bi wani tsari da ba Alqur’ani ba, sai ya zamana mu ne ma muke taimakon wannan tsarin da ya yi hannun riga da na Allah Ta’ala, dokokinsa suka saba da dokokin Allah Ta’ala, ta yaya Allah zai dube mu alhali mun butulce masa!?


Muna kira ga masu budaddiyar qwaqwalwa, ma’abota 

‘yancin tunani, masu neman kubuta duniya da lahirar su, su cire batun ra’ayi da sabaninsa, su natsu su nazarci wadannan 

jawaban na Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), haqiqa mafitarmu ba shi a ko’ina in ba a 

cikin littafin Allah da koyarwar ManzonSa (S) ba.


Naqaltuwa Freedom Fighters Ng, daga littafin Najeriya Ina Mafita, wallafar cibiyar Wallafa.

Post a Comment

1 Comments