Ankarbe Ikon Karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya daga Hannun Kasar Indonesia.

 


Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta kwace ikon  karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta maza 'yan kasa da shekaru 20 a hannun kasar Indonesia da zata gudana karshen wannan shekarar bayan da wani jami'in kasar Indonesia ya nuna rashin amincewarsa da halartar tawagar 'yan wasan Kasar 'yan wariyar launin fata ta "Isra'ila".


"FIFA ta yanke shawarar ne, saboda yanayin da ake ciki, don cire Indonesia a matsayin mai masaukin baki na FIFA U-20 World Cup 2023," in ji FIFA a cikin wata sanarwa, ba tare da bayar da karin haske ba. "Za a sanar da sabon mai masaukin baki da wuri-wuri, tare da kwanakin gasar a halin yanzu ba a canza ba."


Sanarwar ta ce, ana kuma iya sanyawa hukumar kwallon kafa ta Indonesiya (PSSI) takunkumi.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Wayan Koster, gwamnan tsibirin shakatawa na Bali, ya aike da wasika ga ma'aikatar wasanni ta Indonesiya yana neman a hana "Isra'ila" shiga gasar a lardin."


Gwamnan Bali ya kuma bayyana a cikin wasikar cewa gwamnatin lardin Bali ta ki yarda da tawagar 'Isra'ila' su shiga gasar a Bali.


Indonesiya, kasa ce mai rinjayen musulmi da ke da mutane sama da miliyan 270, tana goyon bayan al'ummar Palasdinu.


Sun ki amincewa da duk wani aiki na daidaitawa da "Isra'ila", masu zanga-zangar Indonesiya sun yi macin (Marching)  a farkon wannan watan a Jakarta babban birnin kasar suna neman gwamnati ta haramtawa kungiyar ta Isra'ila wasa a gasar.

Post a Comment

0 Comments