Kungiyar Mayakan Palasdinawa ta Hamas ta gargadi Isra'ilar neh akan hana falasdinawan shiga Masallacin Qudus din a cikin watan Ramadan mai albarka tareda korarsu a masallacin mai tsarki.
"Muna gargadin gomanatin mamayar HKI akan farmakar maziyarta da masallata a masallacin" kamar yanda babban Jami'in Hamas Isma'il Ridwan din ya fada a wata hirarsa a daren ranar Talata.
Ya kara da cewa "Mayakan gwagwarmayar suna bibiye da yanayin da masallatan Al-Aqsa din suke ciki a kowane lokaci don kasancewar Masallacin guri na uku mafi daraja, tabbas zamu kare Al-Aqsa mai tsarki.
A daren ranar Assabar 'yan sandan Israilar masu yawa sun farmaki gaban Al-Qiblar masallacin inda suka tarwatsa musulmin dake Ibada a gurin.
A wani faifan Bidiyo ya nuna yanda masallatan Maza da Mata suke kwalla Kabbara ga 'yan sandan lokacin da suke kokarin tarwatsasu daga cikin ginin masallacin.
An hana falasdinawan shiga Masallacin tareda rufe kofofin shiga Masallacin kamar yanda wani rahoton falasdinawan ya nuna.
Wata daukar video ta nuna yanda rundunar 'yan sandan suke farmaka tareda kama falasdinawan dake Ibada a gurin.
Mai magana da yawun Hamas din Muhammad Hamadeh, yayi Allah wadai da faruwar lamarin da kuma nuna bacin ransa akan cigaba da zalintarda 'yan mamayar keyi a tsohon garin na Al-Quds dake karkashin kulawar sojin mamayar HKI.
Hamadeh ya janye yarjejeniyar da ke tsakaninsu da masu kishin Yahudawa da 'yan sandan Isra'ilar kan kara lokutab shigowa masallacin Al-Aqsan ,ya kara da cewa "irin wannan shirine da yunkuri na mamaye masallacin da kuma neman samun cikakkiyar iko da Masallacin na Qudus" wannan yunkurin bazai taba canja tarihi da qimar masallacin a fiskar musulinci.
Ya kara da kira ga Palastinawan dake zaune a yankin gabar tekun Jordan da kuma mazauna gurinda Isra'ila din ta mamaye a 1948 su tsaya don cigaba da adduo'insu da Ibadu don farfado da martabar musulmi kuma su tsayu kyam akan fatattakar 'yan mamayar dake yunkurin canja tarihi.
Hardline ta Isra'ila suna farmakar masallacin na Al-Aqsa akowaneh rana, matakinda yayi matukar fusata falasdinawan kan irin yanda 'yan sandan cikin Tel-aviv ke bada kariya ga masu mamayar a cikin garin.
An baiwa Yahudawan damar kai ziyara a masallacin dukda wadanda ba Musulmi ba basu da damar gabatar da kowane nau'in Ibada a farfajiyar masallacin kamar yanda wata yarjejeniyar da akayi tsakanin Telaviv da gomnatin Jordan a cikin Farkawar da Israilar tayi a 1967.
0 Comments