Gabanin fara kidayar shekarar 2023, hukumar kidaya ta kasa a ranar Larabar da ta gabata ta ce ba za ta yi tambayoyi masu alaka da addini ba.
A wata sanarwa da Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Isiyaka Yahaya ya fitar a ranar Laraba, Hukumar ta ce an dauki matakin cire addini tare da kabilanci a cikin takardar kidayar jama’a, anyi la’akari da irin muhimman batutuwan da suka shafi siyasar Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa bukatar ceto bayanan kidayar daga gardama da tashin hankali zai sa hukumar NPC ta kaucewa tambayoyin da suka shafi addini.
"Don kauce wa shakku, Hukumar na son bayyana babu shakka cewa kidayar yawan jama'a da gidaje na shekarar 2023 ba za ta haifar da tambayoyi kan addini ba."
Hakan na zuwa ne a cikin wani faifan sauti na WhatsApp da ke ikirarin cewa za a baje kolin addinin mutum. An shirya atisayen ne a ranar 3 ga Mayu.
0 Comments