-Sayyed Zakzaky
Na'am, a nan Allah ya yi mana halitta yadda ya so, shi ya ba mu siffofinmu, yadda duk muka ga kanmu haka Allah ya yi mu, haka Allah ya ga daman yi.
To amma gobe kiyama Allah zai canza mana halitta, zai ba mu wata siffa, za ta yi kama da tamu din nan, amma kuma za ka sami tasirin ayyukanmu bayyane a cikin siffofinmu, masu kyawawan ayyuka za su zama kyawawa, masu munanan ayyuka za su zama munana.
A nan nakan ga masu zane sukan yi wani abu, kun san wani abu da ake ce wa 'Catoon', a jarida akan zana abu kamar wata halitta ta daban, wato abin da mai zanen yake nufi, yana nufin ya nuna mummunar dabi'ar
mutumin da ya zana din ne.
Za ka ga wadansu mutane suna yin wannan irin 'Catoon' din. Akan nuna wani a talabijin, wani akan sa a jarida, da ma galiba a jaridu aka fi zanawa, sai ka ga sun yi mutum sun kamanta shi da wani abu.
Alal misali na taba ganin an kamanta wasu mutane guda biyu, daya aka yi masa qoqon Kunkuru a baya, daya kuma aka yi masa katantanwar Dodon Kodi a bayansa, sai aka nuna shi Kunkurun shi ne shugaban kasa, Dodon Kodin kuma shi ne mataimakinsa.
Sai ana cewa yana ce masa "ka yiwo sauri tafiyar fa na da nisa."` Wato suna nufin cewa su wadannan mutane suna tafiya dikin-dikin, wato sun ki su yi tafiya, amma in ka gani za ka gane su sosai, da ganin hular shi Kunkurun ka san wanene. Daga ganin kuma sifar shi (mataimakin) za ka gane shi.
Wato dai abin da nake kokarin in ce shi ne, ka ga a nan suna zana mutum, amma da ka gani za ka gane cewa wane ake nufi, duk da sun yi masa mummunar kama, ko da sun kamanta shi da Alade ne ko Kare, in dai wane suke nufi, da ka gani za ka gane cewa wannan wane ne.
To wannan shigen irin wannan kenan, Ka ga a nan ma dan Adam yana yi, to ballantana Allah Mahallici, Allah Ta’ala yana iya yin Alade mummuna ko Jaba mummuna, amma mutanen da suka san mutumin a duniya in suka hango shi za su ce wancan wane ne, in sun gan shi a gidan wuta, za su ce wane ne ga shi can amma an yi masa halittar Gursunu.
Da za a yi mutum a Aljanna shi kuma a yi shi mai kyau, a yi shi kyakkyawan gaske, Ko yaya ya kasance a nan duniya (saboda muni), to in ka gan shi za ka ce wane ne, amma yanzu ya zama kyakkyawa. Wato Allah Ta’ala zai iya ba shi siffarsa ta duniya da kyakkyawar kama.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.
TSOKACI:
Mukaddara wannan mutumin yana da kyawun halitta da hancinsa mai kyau da gashinsa mai kyau, kuma mutum ne mai tsafta, rigunansa fesfes.
Amma da aka zauna da shi sai aka ga mai mugun hali ne. Bari mu ce alal misali da aka zauna da shi sai aka gane cewa shi barawo ne, yana dauke-dauke.
To ranar da ya zo fes-fes da kyakkyawan tufar nan tasa yana gabatowa, a ranka wa kake ganin yana zuwa? barawo kake gani! Ka ga a nan kyawunsa ya zama abin da Bahaushe ke ce wa kyawun dan maciji.
Saboda yanzu ba kuma kyawun kake gani ba, mummunar dabi'arsa kake gani, Ka ga wannan ashe ya nuna maka dabi'a ita ce mutum”. “Gobe kiyama Allah zai canza mana halitta, zai ba mu wata siffa, za ta yi kama da tamu din nan, amma kuma za ka sami tasirin ayyukanmu bayyane a cikin siffofinmu.
Masu kyawawan ayyuka za su zama kyawawa, masu munanan ayyuka za su zama munana.
“Kun san wani abu da ake ce wa 'Cartoon', a jarida akan zana mutum a kamanta shi da wani abu daban, (kamar Kunkuru ko Dodon
Kodi)…amma da ka gani za ka gane cewa wane ake nufi, duk da sun yi masa mummunar kama. Ko da sun kamanta shi da Alade ne ko Kare, in dai wane suke nufi, da ka gani za ka gane cewa wannan wane ne.
To wannan shigen irin wannan kenan, ka ga a nan ma dan Adam yana yi, to ballantana Allah Mahallici!
Naqaltowa Freedom Fighters Ng, daga littafin Tasirin Dabi'u Na Sayyed Zakzaky, wallafar cibiyar Wallafa da yada ayyukan Sayyed Zakzaky (H).
0 Comments