- Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)
Abin da nake kokarin in nuna a nan shi ne halin da muka riga muka shiga ayyuka ne na hannuwanmu. Kuma a nan babban laifin da ya janyo wannan bai wuce kangare wa Allah Ta’ala da aka yi ba.
Domin ta yiwu mutum ya ce, to yaya mu za mu sha wahala saboda fandara daga bin tafarkin Allah, su ko kasashen kafirai suna jin dadi? Sai mu ce, ai su (kafirai) ba su yi ma Allah karya ba, su ba su ce suna son Aljanna ba ballantana ma su sa rai da ita.
Ba su kuma yi wa Allah karyan Musulunci ba, Kafirai suke, sun kafirce wa Allah kuma duniyar ta yi masu, aljannarsu suke ci, tsakanin su da wuta mutuwa.
Saboda haka ko an sakar masu (duniyar), wannan ya yi daidai, kamar yadda aka ce duk lokacin da Allah Ta’ala ya aiko Manzo yakan takura mutane, har idan sun wa'aztu shi kenan, idan kuma ba su wa'aztu ba akan yi masu ‘Istidraji’ har ranar kamun karshe.
To muna iya cewa,
su kasashen kafirai an yi masu Istidraji, an saka masu. su duniyar suka sani, ba su da sauran su koma wa Allah, tunda dai ba su yi masa karya ba.
To, amma ina ga mutumin da ya bude bakinsa ya ce shi ya yi imani da Allah, ya kuma ce ya yi imani da Manzon Allah, ya kuma ce ya yi imani da abin da Allah ya saukar wa Manzon Allah, amma a ayyukansa da zantukansa ya kangare wa Allah.
Da kuma littafinsa, a lokaci guda kuma yana neman taimako daga wajen wadanda suka yi wa Allah tawaye? A nan wanene babba? Da wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa da
littafinsa, amma ya kangare, yake neman taimako wajen Ibilis; da shi da Ibilis wanne ya fi ci gaba? Ka ga da ma Ibilis dan tawaye ne.
To ko, dole wanda ya fandare, ya kuma je wajen fandarraru yana neman gudummawa matsayinsa ya fi wulaqantuwa. Dole ne musulmin da ya sa kansa cikin wannan
hali, kafiri ya fi shi, don shi kafiri bai yi wa Allah karya ba.
Don haka ba mamaki irin kasashen da ake cewa sun ci gaba, suke take kasashe suna murjewa kuma suna tatse arziki su yi waje da shi, ana biye da su tare da kyakkyawan ikhlasi da bauta don su zo su ciyar da kasa gaba.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.
Naqaltowa Freedom Fighters Ng, daga littafin Najeriya Ina Mafita, wallafar cibiyar Wallafa da yada ayyukan Sayyed Zakzaky (H).
0 Comments