NASIHAR SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) GA MALAMAI MASU TAFSIRI!

 


"Muna cewa ya kamata a girmama Alkur’ani, in mutum yana da ra'ayi, kamar na siyasa ko dangane da wani abu, ya kamata ne ya samu wani lokaci ya yi lakca, a daidai wannan lokacin sai ya fadi wadannan ra'ayoyin nasa a ji, amma ba a lokacin da yake Tafsirin Alkur’ani ba." 


 Ko kuma in ana Tafsirin Alkur’ani ba laifi a ajiye Alkur’anin a yi wasu bayanai da suka shafi al'umma wadanda ake ganin ya dace su ji, kamar sanarwar janaza ko neman addu'a, ko sanarwowi ko amsa tambaya, ko abin da ya yi kama da haka, amma ya zama ba a cikin Tafsir ba. "Amma bai kamata a ja baki, sai mutum ya buge da fadan wasu ra'ayoyi na ƙashin kansa ba. Ya ji tsoron Allah, kar ya zama ya mai da Alkur’ani kayan wasa."


 "Ma'anar Tafsiri shine a bayyana muradin mai magana, kuma wannan mai maganar shine Allah Ta'ala, me Allah yake nufi da fadin wannan magana? Abin da kake cewa kenan in kana Tafsiri. 


Don haka ko da wani ne ya yi magana, sai ka fassara shi ba daidai ba, ai baka yi adalci ba, ballantana ace wannan mai maganar Allah Ta'ala ne, sai ya zama kana fadin Maganar Allah Ta'ala, amma kana fadin ra'ayinka."


Manzon Allah (S) yana cewa: "Wanda ya fassara Alkur’ani ba da ilimi ba ya saurari makomarsa a wuta." da kuma cewa: "Wanda ya fassara Alkur’ani da ra'ayinsa ya saurari makomarsa a wuta."


@SZakzakyOffice

04/04/2022

Post a Comment

0 Comments