- Sayyed Zakzaky (H)
Kullum kamar yadda nakan tunatar da mu kan cewa shi fa ambato ko tunatarwa ko wa'azi, tamkar abinci ne ga ruhin dan adam, Ruhin dan Adam yana rayuwa ne da zikiri da ilimi.
Wadannan abubuwa biyu su suke rayar da shi, kamar yadda gangan jiki ke rayuwa da cin abinci da shan ruwa, kamar yadda mutum ya san cewa ba zai ci abinci ya gama ba, ya zama shi kenan ba zai sake ci ba.
Kullum in dai yana da rai, shi mabukaci ne ya dinga cin abinci, Haka kuma misali jikinsa mabukaci ne ga wanka, ba zai yi wanka ya gama ba, ko da kuwa zai wanke jikinsa da ruwan kogi ne a lokaci guda, to in aka kwana zai bukaci ya sake yin wani wanka din.
Saboda haka ba wani abu ne wanda mutum zai yi ya gama ba, haka kuma wanki shi ma, ba za ka wanke suturarka rana daya, a ce bari
ka yi masa wanki ya fita fyes sai badi kuma ba, matukar za ka sa, za kuma ka bukaci ka sake wanke shi.
To, haka nan ruhin mutum yake dangane da ilimi da zikiri, shi mabukaci ne gare su da'iman sarmadan, kullum yana ta dada kara ilimi ne, yana kuma dada kara zikiri ne.
Don haka ne ma Allah (T) ya sanya
mana zikirori wajibai guda biyar a kowace rana, Khamsu Salawat kenan.
Wanda har Manzon Allah (SAW) yake kwatanta su da kamar mutum ne wanda da akwai kogi kusa da dakinsa yana wanka sau biyar kowace rana, ya ce za a sami dauda a tare da shi? Aka ce a'a. Ya ce to kamar haka ne.
Wadannan lokuta ne da aka ba ka dama ka ba ruhinka nasa abinci din, kun ga wato ruhi mabukaci ne ma ga abinci fiye da gangan jiki, tunda da za a ce wani mutum yana cin abinci sau biyar a rana, za a ce masa Acici, za a ce ya cika cin abinci.
Bil hasali ma dai shi wajen tarbiyyar ruhi ma ana rage cin abinci din, wato ana cin abinci daidai gwargwadon bukatar jiki ne, kuma har a dan yi wa jikin tarbiyya da ya dan sha wahala ya manta abincin na dan wadansu lokuta.
Don haka nan ma akan sa azumi, idan jiki ya dan ji yunwa ya dan ji wahala, ruhi yana amfana,
to shi kuwa ruhi ba a shagaltar da shi da wani abu, shi zikirin kawai ake ta ba shi, ba a gafalantar da shi da wani abu da zai manta zikirin.
In da mutum zai kasance da'iman yana ta zikirullahi ne, to falillahil-hamdu.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.
Naqaltuwa Freedom Fighters Ng, daga littafin Tasirin Dabi'u Na Sayyed Zakzaky, wallafar cibiyar Wallafa da yada ayyukan Sayyed Zakzaky (H).
0 Comments