- Shugaban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Mohammad Hossein Baqeri ya yaba da yadda kasar Iran ke kara samun karfin fada a ji da kuma juriya, ya ce ci gaban da ake samu a shiyya-shiyya da na kasa da kasa yana kara kusantar Amurka da gwamnatin sahyoniyawan zuwaga rushewa.
Babban Janar din na Iran ya yi wannan tsokaci ne a ranar Litinin din da ta gabata, inda ya ce: Shekarar da ta gabata (kalandar Iran) (wanda ta kare a ranar 20 ga Maris) ta kasance wani yanayi mai cike da tashe-tashen hankula a lokacin da sojojin (Iran) suka dauki manyan matakai na karfafa karfin kariya da kuma shirye-shiryensu.
“Abin da mutum yake gani a matakin duniya da na yanki… shine ci gaban Iran a duniya da yankin gabas ta tsakiya suna raunana girman kan duniya da kuma tura gwamnatin sahyoniya ga rugujewa…” in ji shi, Press TV ta ruwaito.
Baqeri ya jaddada cewa da yawa daga cikin masu tunani na Amurka da ma 'yan siyasa sun yarda da wannan lamari kuma har ma shugaban wannan gwamnatin ta karya ya sha nanata cewa Isra'ila na gab da rugujewa...
Wannan shi ne alkawarin Jagoranmu (Ayatullah Sayyid Ali Khamenei). cewa ba za su ga shekaru 25 masu zuwa ba."
A watan Fabrairu, shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya yi gargadin abin da ya ce rikici na gabatowa da ma yiwuwar zubar da jini, yana mai cewa Tel Aviv na gab da rugujewa, wato al'ummar dakum tsarin mulkin.
Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da yankunan da aka mamaye ke fama da zanga-zangar makwanni 13 da suka gabata a jere kan wani kunshin "sauye-sauyen shari'a" mai cike da cece-kuce da rashin amincewa da shi. Wanda da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gabatar.
Zanga-zangar ta kasance wani shiri ne na mako-mako tun daga karshen watan Disamba, lokacin da firaministan ya bayyana aniyarsa ta aiwatar da sauye-sauyen.
Netanyahu ya yi iƙirarin cewa sauye-sauyen da ake zargin suna da nufin sake daidaita madafun iko tsakanin bangaren zartarwa na gwamnati da na shari'a ta hanyar hana kotun koli ta soke hukuncin da ta yanke. Har ila yau suna neman baiwa ‘yan majalisar babban iko a kwamitin da ke zaban alkalai.
Masu adawa da Netanyahu na kallon yunkurin da majalisar ministocinsa ta yi na zartar da dokar kan abin da ake kira sauye-sauye a matsayin barazana ga 'yancin cin gashin kan kotun kolin, suna masu bayyana hakan a matsayin "juyin mulki." Suna kuma zargin Netanyahu da kokarin yin amfani da sauye-sauyen don soke hukuncin da za a yanke masa a yayin da ake shari'a kan laifuka uku na cin hanci da rashawa.
Bayan zanga-zangar makwanni da aka shafe ana tafka ta’asa a wasu lokutan, a karshe firaministan Isra’ilan ya amince da jinkirta shirinsa na sake fasalin shari’a.
0 Comments